'Yan Sanda Sun Dakile Shirin Masu Garkuwa da Mutane, Sun Cafke Miyagun Masu Laifi

'Yan Sanda Sun Dakile Shirin Masu Garkuwa da Mutane, Sun Cafke Miyagun Masu Laifi

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Sabon Gari Lassa, karamar hukumar Askira, jihar Borno, a wani yunkuri na yin garkuwa da mutane
  • 'Yan bindigar sun dira gidan wani mazaunin garin, Mohammed Abubakar, amma ya nuna turjiya, lamarin da ya sa suka tsere da gudu
  • Sai dai, ba su yi tazara ba, jami'an 'yan sanda suka cimma su, inda suka yi nasarar cafke mutum uku daga cikin masu garkuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Wasu gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a Sabon Gari Lassa, karamar hukumar Askira, jihar Borno.

Sai dai rana ta bace wa 'yan bindigar, inda suka yi karan batta da jami'an rundunar 'yan sansan Najeriya reshen jihar.

Rundunar 'yan sandan Borno ta dakile yunkurin sace muta ne a karamar hukumar Askira
Rundunar 'yan sanda ta dakile harin 'yan bindiga a jihar Borno. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da yankunan Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya sanar da hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun sace sakataren karamar hukuma da wasu mutum 4 a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan Borno sun dakile harin masu garkuwa

Zagazola Makama, ya shaida cewa:

"Rundunar 'yan sandan Borno, ta dakile wani harin sace mutane a Sabon Gari Lassa, karamar hukumar Askira Uba."

Hakazalika, rahoton ya nuna cewa rundunar ta samu nasarar cafke mutum uku daga cikin miyagun da suka kai wannan farmakin.

Sannan kuma, 'yan sandan sun kwato bindiga kirar 'pistol' da aka kera ta a nan gida Najeriya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Magidanci ya fatattaki masu garkuwa da mutane

Majiyoyin tsaron sun shaida cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairun 2025.

An ce 'yan bindigar sun dura gidan wani Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin yin garkuwa da shi.

Sai dai, Malam Mohammed Abubakar ya nunawa 'yan bindigar turjiya tare da mayar da martani da adda, lamarin da ya tilasta miyagun tserewa.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah

'Yans andan Borno sun cafke 'yan bindiga 3

Majiyoyin tsaro sun yi bayanin yadda 'yan bindiga suka farmaki wani kauyen Borno
'Yan sandan Najeriya sun cafke 'yan bindiga da suka kai harin garkuwa da mutane a Borno. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 6:00 na safiyar Juma'a, tawagar 'yan sanda da 'yan sa-kai sun kai dauki, tare da bin sahun 'yan ta'adda.

An ce jami'an tsaron sun gano mabuyar 'yan ta'addar a bayan gari, inda suka samu nasarar cafke miyagu uku: Salisu Hussain, Buhari Hussaini da Umar Bello.

Rahotanni sun bayyana cewa dukkanin wadannan miyagun uku da aka kama, sun fito ne daga garin Gajali da ke karamar hukumar Askira Uba.

'Yan sanda sun aika sako ga mutanen Borno

Rundunar 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran wadanda suka kai harin, yayin da aka kwato bindigar 'pistol' 'yar hadin gida.

Rundunar 'yan sandan Borno ta jinjinawa jami'anta da na 'yan sa-kai bisa gaggawar kai daukin da suka yi da har ya sa aka kama miyagun uku.

Hakanan, rundunar ta bukaci mazauna yankunan da su kasance masu sa ido kan shige da fice a garuruwansu, tare da kai rahoton duk motsin da ba su yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun farmaki maboyar wani babban dan bindiga, an kashe 'yan ta'adda 53

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sandan jihar Katsina sun kai daukin gaggawa bayan samun rahoton harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan matafiya a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sandan sun dakile harin, wanda 'yan bindiga suka kai a kan matafiya a karamar hukumar Danmusa ta Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel