Karya Ta Kare: Jami'an Tsaro Sun Cafke Babban Mai Sayarwa Bello Turji Makamai a Sokoto

Karya Ta Kare: Jami'an Tsaro Sun Cafke Babban Mai Sayarwa Bello Turji Makamai a Sokoto

  • Jami'an tsaro a karamar hukumar Isa, Sokoto, sun kama Hamza Suruddubu, babban mai samar da makamai ga dan bindiga, Bello Turji
  • Suruddubu yana safarar makamai daga Zamfara zuwa Gabashin Sokoto, yana sayarwa manyan 'yan ta’adda, ciki har da Halilu Buzu
  • Wata majiya ta yi zargin cewa akwai sa hannun jami'an tsaro a safarar makaman da ake yi a yankunan Isa da Sabon Birni, Sokoto
  • Shugabanni da masu ruwa da tsaki sun bukaci hukumomin tsaro su binciki yadda ake safarar makaman da ake amfani da su a yankin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Jami'an tsaro a karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto sun samu gagarumar nasarar gurgunta ayyukan rikakken dan bindiga, Bello Turji.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun cafke Hamza Suruddubu, wani babban mai sayarwa Bello Turji makaman da yake ta'addanci da su..

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake, an zargi ya ƙaƙaba N25m ga yan kauye

Majiyoyi sun yi magana kan hanyoyin da Bello Turji ke samun makamai
Jami'an tsaro a Sokoto sun cafke babban mai safarar makamai ga Bello Turji. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun cafke dillalin makamai, Suruddubu

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya fitar da rahoton a shafinsa na X, yana mai cewa makaman Hamza ne ake ta'addanci da su a yankin Isa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin tsaro sun labarta cewa Hamza Suruddubu, ya kasance rikakken dillalin makamai a Gabashin Sokoto, kuma yana shiga ayyukan ta'addanci.

Majiyoyin sun shaida cewa Suruddubu ya na safarar makamai daga jihar Zamfara zuwa Gabashin Sokoto, inda yake sayarwa manyan 'yan ta'adda.

Suruddubu, mai sayarwa Bello Turji makamai

An ce shi ne babban mai sayarwa hatsabibin dan bindiga, Bello Turji makamai, kuma shi ne ke sayarwa Boka da Halilu Buzu kayan yaki.

Halilu Buzu ya kasance hatsabibin dan bindiga da sojojin Najeriya suka kawo karshensa a watan Satumbar 2024 tare da wasu yaransa.

Bello Turji na ci gaba da addabar jihohin Zamfara, Sokoto
Bello Turji na ci gaba da addabar jihohin Zamfara, Sokoto. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Facebook

Baya ga safarar makamai, bincike ya gano cewa Suruddubu yana kuma samarwa 'yan bindiga kayayyakin more rayuwa, kamar abinci da babura.

Kara karanta wannan

DSS ta gano makamai a ofishin hadimin tsohon shugaban majalisar Legas

Wata majiyar ta bayyana cewa ana zargin akwai sa hannun wasu jami'an tsaro na karamar hukumar Shinkafi a safarar makaman da ke gudana a yankunan.

Ana so hukumomi sun binciki ayyukan Suruddubu

Sai dai, Legit Hausa ba ta iya samun wata hujja da ta tabbatar da wannan ikirari da aka ce majiyar ta yi ba.

Rahoto dai ya nuna cewa shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun nemi hukumomin tsaro sun binciki ayyukan Suruddubu sosai.

Shugabannin na ganin cewa akkwai sa hannun jami'an tsaro da wasu kusoshin yankin a safarar makaman da Suruddubu yake yi a tsakanin Isa da Sabon Birni.

Dan majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan majalisar Sokoto, Hon. Aminu Boza ya yi ikirarin cewa yanzu haka Bello Turji yana zaune a Gabashin Sokoto.

Hon. Aminu Boza ya yi ikirarin cewa Bello Turji ya kakaba harajin ₦25m kan wasu kauyuka da ke makotaka da sabon sansanin da ya yi.

Dan majalisar jihar, ya nemi jami'an tsaro da su tarfa hatsabibin dan bindigar, Bello Turji a yankunan kananan hukumomin Isa da Sabon Birni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel