'Najeriya na da Arziki': OPEC Ta Yi Fallasa a Gazawar Kasar a Fitar da Danyen Mai
- Shugaban Kwamitin Gwamnoni na OPEC, Ademola Adeyemi-Bero, ya ce Najeriya ta fi karfin gangar danyen mai sama da miliyan daya da take fitarwa
- Ya bayyana cewa kasar na da isassun rijiyoyin mai da yalwar arzikin karkashin kasa da za su ba ta damar samar da fiye da ganga miliyan biyu a kullum
- Mista Adeyemi Bero ya ba da tabbacin hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da daga likkafar kasar nan a fannin fitar da danyen mai a idon duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Shugaban Kwamitin Gwamnoni na Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC), Ademola Adeyemi-Bero, ya ce danyen man da Najeriya take fitarwa a kullum ya yi kadan.
Adeyemi-Bero ya bayyana hakan a ranar Alhamis a taron masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur, wanda aka gudanar a Abuja, inda ya kara da cewa kasar na da dimbin arzikin danyen mai.

Asali: Twitter
Jaridar Punch News ta wallafa cewa Mista Adeyemi Bero ya bayyana cewa wadanda ke OPEC na da yakinin cewa Najeriya na iya samar da fiye da adadin ganga miliyan 1.5 da aka kebe mata a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake bayyana abin da ya dace a ce kasar na fitawar, shugaban kwamitin ya ce, bai kamata Najeriya ta rika samar da abin da ya gaza ganga miliyan hudu a kullum ba.
OPEC ta jinjina kokarin Najeriya
The Guardian ta ruwaito cewa Ademola Adeyemi-Bero ya kuma bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta nuna da gaske take, kuma za ta iya idan tana bukatar OPEC ta kara yawan danyen mai da aka ware mata.

Asali: Twitter
Ya ce karin adadin da aka samu a watan Janairu zuwa ganga miliyan 1.7 na mai da ake fitar wa a kullum wata babbar alama ce a kan kokarin da kasar ke yi.

Kara karanta wannan
Amurka ta yi baki biyu, ta musanta zargin dan majalisa kan daukar nauyin Boko Haram
Ya ce:
“Ina ganin abu mafi muhimmanci da ya kamata mu fahimta shi ne, da irin adadin rijiyoyin mai da Najeriya ke da su, bai kamata kasar ta rika samar da kasa da ganga miliyan biyu a kullum ba.
"Najeriya ya kamata ta rika samar da ganga miliyan biyu da rabi, ko uku, ko har miliyan hudu a kullum da irin wannan arziki da take da shi.
“Kuma ina da yakinin cewa ko a OPEC da sauran kasashen duniya, suna da amannar cewa za mu iya yin hakan, amma dole ne mu nuna cewa za mu iya samar da hakan."
Shirin OPEC a kan Najeriya
Da yake magana kan mukaminsa a matsayin Shugaban Kwamitin Gwamnoni na OPEC, ya bayyana cewa OPEC ce ke aiwatar da duk ayyukan da take yi, amma ba ta da ikon amincewa da su har sai an tuntuɓi kwamitin gwamnonin.
A sabon mukaminsa, Adeyemi-Bero ya jaddada cewa dole ne ya yi aiki don ganin an kara wa Najeriya kaso zuwa ganga miliyan 2.1 a kullum.
Ya ce:
“Muna kokarin ganin cewa an kai adadin samar da mai na Najeriya zuwa ganga miliyan 2.1 a kullum.
A matsayina na gwamnan OPEC, aiki na shi ne, tare da hadin gwiwar OPEC a Najeriya, mu tabbatar da cewa an cimma wannan adadi."
OPEC: An shiga fargaba kan matatar Dangote
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun tabbatar da cewa matatar man fetur, mallakin Aliko Dangote na shirin sauya fasalin kasuwar mai ta duniya, musamman a Turai.
Rahoton OPEC na watan Nuwamba 2024 ya bayyana cewa matatar za ta zama barazana ga masana'antar mai da gas, musamman a Arewa maso Yammacin Turai (NWE) da zarar ta fara aiki yadda ya dace.
Asali: Legit.ng