Kasashen duniya sun zabi dan Najeriya shugaban kungiyar OPEC
Masu ruwa da tsaki a majalisar kasashe masu arzikin man fetir ta duniya, OPEC, sun sake zaben dan Najeriya, Muhammad Barkindo a matsayin babban sakataren kungiyar a karo na biyu.
A ranar Litinin, 1 ga watan Yuli ne aka sake zaben Barkindo domin ya zarce akan wannan muhimmiyar kujera na tsawon shekaru uku masu zuwa, kuma zaben ya gudana ne a sakariyar kungiyar dake Vienna.
KU KARANTA: Karan kwana: Uwargida ta jibga ma Mijinta icce, ya sheka barzahu

Asali: Twitter
Baya ga zaben Mohammed Barkindo a matsayin shugabanta, majalisar ta sanar da kara wa’adin watanni tara don cigaba da rage adadin gangar man fetir da yayanta masu arzikin ma fetir suke fitarwa, ta haka ne farashin mai zai yi daraja a kasuwan duniya.
An fara zaben Barkindo ya jagoranci OPEC ne a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2016, kuma dama tun a can baya ya taba shugabantar OPEC a matakin wucin gadi a shekarar 2006, haka zalika ya wakilci Najeriya a majalisar OPEC daga shekarar 1993 zuwa 2008.
Lagit.ng ta ruwaito a shekarar 1959, 10 ga watan Afrilu aka haifi Barkindo a jahar Adamawa, sa’annan ya yi karatun digiri a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, sa’annan ya kara karatu a jami’ar Southeastern dake Amurka, ya kara yin karatun babbar difloma a jami’ar Oxford.
A shekarar 2009 ne tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Umaru Musa Yaradua ya nadashi mukamin shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, mukamin da ya rike zuwa 2010.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng