'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Sace Shugaba bayan Sun Harbe Shi a Abuja

'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Sace Shugaba bayan Sun Harbe Shi a Abuja

  • Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kungiyar matasan Afenifere na kasa, Eniola Ojajuni a babban birnin tarayya Abuja
  • Sakataren kungiyar, Abiodun Aderohunmu ya ce masu garkuwar sun kira iyalansa, sun nemi a haɗa masu kuɗin fansa Naira miliyan 100
  • Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen ceto shi cikin ƙoshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙungiyar matasan Afenifere, Eniola Ojajuni, a birnin tarayya Abuja.

Sakataren kungiyar matasan, mai fafutukar kare al'adun yarbawa a Najeriya, Abiodun Aderohunmu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Eniola Ojajuni.
Yan bindiga sun sace shugaban kungiyar matasan Afenifere a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A cewar Aderohunmu, miyagun sun sace Ojajuni ne a ranar Litinin, 12 ga Fabrairu, 2025, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun nemi fansa N100m

Ya ƙara da cewa bayan sace shugaban matasan, masu garkuwar sun nemi a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 100 kafin su sake shi.

Aderohunmu ya bayyana cewa an harbi Ojajuni a katararsa a lokacin da ‘yan bindigar ke kokwawar tafiya da shi, lamarin da ya janyo masa munanan raunuka.

"Mun yi matukar girgiza da jin labarin cewa an sace shugabanmu, kuma an harbe shi a sassan jikinsa kafin a tafi da shi.
"Masu garkuwar sun kira iyalansa kuma sun nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa,” in ji shi.

Sakataren kungiyar ya buƙaci ƴan Najeriya da su sa shugabansu addu'a ttare da fatan Allah ya buɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya

Sai dai bai yi ƙarin haske kan halin da ake ciki game da bukatar masu garkuwa na biyan kuɗin fansa ba kuma babu ani bayani daga iyalan wanda aka sace.

Kara karanta wannan

Muhimman dalilai 4 da suka karya farashin abinci ana shirin azumin Ramadan

An bukaci jami'an tsaro su tashi tsaye

Kungiyar matasan Afenifere ta yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don ganin an sako Ojajuni ba tare da wata matsala ba.

“Muna kira ga gwamnati da dukkan hukumomin tsaro da su shiga cikin wannan lamari don ganin an sako Ojajuni cikin koshin lafiya,” in ji Aderohunmu.
Yan sanda.
Mahara sun nemi N100m a matsayin kudin fansar shugaban matasan kungiyar Afenifere Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa har yanzu ba ta su samu rahoton sace shugaban matasan a hukumance ba.

Duk da haka ta tabbatar da cewa rundunar ƴan sanda za ta gudanar da bincike kan lamarin kuma ta ɗauki matakin da ya dace.

Sace mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, musamman a yankunan da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Ƴan bindiga sun afka masallaci

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki masallaci a yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Maharan sun afka wa masallacin ne a lokacin da jama’a ke tsaka da yin sallar Asuba, inda suka yi awon gaba da wasu daga cikin masu ibada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262