Ana Tsaka da Farautar Bello Turji, Shugaban Sojojin Najeriya Ya Dura Jihar Zamfara

Ana Tsaka da Farautar Bello Turji, Shugaban Sojojin Najeriya Ya Dura Jihar Zamfara

  • Shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya kai ziyarar aiki ta a Zamfara tun bayan nadinsa, a ranar 30 ga Oktoba, 2024
  • Oluyede ya karɓi bayanai daga manyan kwamandojin soji kan nasarorin baya-bayan nan da matakan dakile ‘yan ta'adda a jihar Zamfara
  • Shugaban sojojin zai gana da dakarun rundunar don karfafa musu gwiwa da kuma tabbatar da ci gaba da yaki da miyagu, irinsu Bello Turji

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya kai ziyarar aiki a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a ranar Alhamis.

Wannan ita ce ziyara ta farko tun bayan nadinsa a ranar 30 ga Oktoba, 2024, yayin da sojoji ke yaki da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya fallasa inda Bello Turji yake, an zargi ya ƙaƙaba N25m ga yan kauye

Shugaban sojojin Najeriya ya kai ziyarar farko Zamfara don duba halin tsaro a jihar
Shugaban sojojin Najeriya ya dura Zamfara domin karfafawa sojoji gwiwar yaki da ta'addanci. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Shugaban sojojin Najeriya ya ziyarci Zamfara

Oluyede ya fara ziyarar ne da duba rundunar tsaro a barikin sojoji, sannan ya karɓi bayani daga kwamandan rundunar, Manjo Janar Oluyinka Soyele, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron yana mayar da hankali kan halin tsaro a yankin, nasarorin baya-bayan nan da matakan da ake dauka don dakile ta’addanci a Zamfara.

Rundunar sojoji na amfani da Operation Fasan Yamma don dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma, inda matsalar garkuwa da mutane ke karuwa.

Laftanar Janar Oluyede ya karfafi sojoji

Shugaban sojojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede
Laftanar Janar Olufemi Oluyede, shugaban sojojin Najeriya ya ziyarci Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ziyarar Laftanar Janar Olufemi Oluyede ta kara nuna kwazon sojoji na kawo karshen 'yan ta'adda, irinsu Bello Turji daga jihohin Arewa maso Yamma.

An ce shugaban sojojin zai kuma kai ziyara zuwa Hedikwatar Brigade ta Daya da ke Gusau domin duba ayyukan sojojin dake fagen fama.

Oluyede zai gana da dakarun rundunar don karfafa musu gwiwa da kuma tabbatar da goyon bayan sojoji wajen yaki da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

Sojoji sun fara bin diddigin Bello Turji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ce dakarunsa na bin Bello Turji kuma za a murƙushe shi nan ba da daɗewa ba.

Oluyede ya ce rundunar soji ta riga ta kawar da shugabannin ‘yan bindiga da yawa a Arewa maso Yamma, yana mai jaddada ci gaba da yaki da ta’addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.