Jami'an Tsaro Sun Bankaɗo Jihar da Fitinannen Ɗan Ta'adda Ya Fake a Arewa
- Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa Jan Kare ne ke jagorantar hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na Jihar Katsina
- Ana zargin cewa yana amfani da dajin Tsaskiya da ke Safana LGA a matsayin maboyarsa, tare da jagorantar garkuwa da mutane da satar dabbobi
- Jami’an tsaro na kara matsa lamba don rusa sansanonin ‘yan bindiga da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa
- Operation Show No Mercy, da aka kaddamar kwanan nan, na samun gagarumar nasara, inda aka rusa sansanonin ‘yan bindiga da dama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Majiyoyin tsaro sun gano cewa Jan Kare, shahararren shugaban ‘yan bindiga, na daga cikin manyan masu shirya hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na Jihar Katsina.
An bayyana cewa Jan Kare na gudanar da ayyukansa ne daga dajin Tsaskiya da ke karamar hukumar Safana, inda yake jagorantar wata babbar kungiya ta ‘yan ta’adda masu dauke da makamai.

Asali: Twitter
Shahararren mai fashin baki kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X cewa Jan Kare na da alhakin hare-hare masu muni garkuwa da mutane, da kuma satar shanu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yankunan da Jan Kare ke aikata ta’addanci
Ayyukan ta’addancin Jan Kare sun daidaita rayuwar jama’a a kananan hukumomin Danmusa, Safana, Dutsin-Ma, Kurfi, da Matazu, inda ake zargin yana tilasta wa mazauna yankunan biyan haraji.
A halin yanzu, jami’an tsaro na kara matsa lamba don rusa cibiyoyinsa da kuma maido da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Hukumomi sun bukaci mazauna yankunan su bada sahihan bayanai da za su taimaka wajen cafke shi da zarar sun gano takamaiman inda yake.
An kaddamar da sabon farmaki kan ‘yan ta'adda
A gefe guda, sabon shirin yaki da ‘yan bindiga mai suna Operation Show No Mercy da aka ƙaddamar a Arewa maso Yamma na ci gaba da samun nasarori, inda an rusa maboyar ‘yan ta’adda da dama.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da sojojin Najeriya suka jaddada kudirinsu na kawo karshen ‘yan ta’adda da kuma ayyukansu a Arewacin Najeriya.
Tun a ƙarshen shekarar 2024 ne shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin tsaro da su tabbatar an kawo ƙarshen miyagun ƴan ta'adda a ƙarshen 2025.
Ƴan ta'adda sun kai hari Adamawa
A baya, mun wallafa cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama da ke Yola, inda suka sace mutane hudu, ciki har da wani jami'in lafiya.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na safe a kauyen Mayo Kila, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, a ƙaramar hukumar Jada, lamarin da ya bar mazauna yankin a cikin rudani da firgici.
Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an tura jami'an tsaro nan take bayan samun kiran gaggawa domin ceto wanda aka sace.
Asali: Legit.ng