Gwamna Abba Zai Jiƙa Mutanen Kano da Ayyukan Alheri, Ya Ware Sama da Naira Biliyan 30
- Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 33.45 domin aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa da inganta ilimi, kiwon lafiya da walwalar jama'a
- Gwamna Abba ya amince da ware waɗannan kuɗi domin aiwatar da ayyukan ci gaba a taron Majalisar zartarws ranar Laraba
- Ayyukan da za a yi da kudin sun haɗa da gina tituna, asibiti, makarantu, gidaje da sauransu duk da nufin inganta rayuwar kanawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da ware Naira biliyan 33.45 domin aiwatar da manyan ayyuka.
Ayyukan da gwamnatin Kano za ta yi da waɗannan kudi sun ƙunshi gina ababen more rayuwa, inganta harkonun ilimi, lafiya, da walwalar al’umma.

Asali: Facebook
Kwamishinan labarai da harkokin cikin gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar zartarwa, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da daraktan harkoki na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai, Sani Abba Yola, ya fitar, an bayyana yadda za a tura kudaden zuwa manyan fannonin ci gaba.
Gwamna Abba zai zuba ayyuka a Kano
Gwamnati ta ware N426.4m domin biyan hakkokin masu share titi 2,369 na tsawon wata tara, karkashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi.
An kuma ware N109m da za a yi amfani da su wajen sayen JAMB ga ƴan asalin Kano, tare da daukar nauyin rajista da horo ga daliban da suka cancanta.
Sai kuma N284.1m da za a gina sabon asibiti na zamani a yankin Rimin Zakara, karamar hukumar Ungoggo.
Har ila yau gwamnatin Kano ta cire N434.3m domin gyaran makarantar sakandare ta 'yan mata (GGSS) da ke Shekara da N893.1m da za a yi gyaran kwalejin Magwan.
Ta kuma ware wasu N90.7m domin gina gidaje guda takwas masu ɗakunn kwana biyu-buyu da gyaran katanga da ofishin bakin kofa a gidan gwamnati.
Sai kuma N6.6bn aka ware domin ayyukan mazabu na 2025 da kuma N256.7m da aka amince da su domin gyaran ofishin mataimakin Gwamna.
Bugu da ƙari, majalisar zartarwar ta amince a futar da N160m domin sayen wani gida a unguwar Ja’en da ke ƙaramar Gwale, don mayar da shi makaranta ta gwamnati.

Asali: Facebook
Gwamnatin Kano za ta gina gidaje 1000
Sannan an ware N5.22bn domin gina gidaje 1,000 masu ɗakuna biyu-buyu, waɗanda za a rabawa mutanen da ambaliyar ruwan bana ta yi wa illa.
Gwamnatin Kano ta kuma ƙara cire N9.76bn domin gina sababbin tituna bakwai a yankunan karkara, tare da gyaran wasu tituna karkashin shirin hanyoyin karkara da kasuwanci na noma (RAAMP - Phase II).
Gwamnatin Kano ta ce wadannan ayyuka da sauransu da za su laƙume N33.45bn za su taimaka wajen inganta rayuwar al'umma da bunkasa ci gaban jihar.
An gano yada kuɗin Kano ke sulalewa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta gano asusun wasu tsofaffin jami'anta da aka yi amfani da su wajen wawure kuɗaɗen shiga.
Hukumar tattara haraji ta Kano watau KIRS ce ta gano asusun bankunan, inda ya koka kan ɓatar makudan kudin da ya kamata gwamnati ta yi amfani da su.
Asali: Legit.ng