NNPP Ta Yi Babban Rashi, Ƙusa a Jam'iyyar Kwankwaso Ya Koma APC

NNPP Ta Yi Babban Rashi, Ƙusa a Jam'iyyar Kwankwaso Ya Koma APC

  • Yusuf Galambi, dan majalisa mai wakiltar Gwaram a Jihar Jigawa, ya bar NNPP ya koma APC, bisa wasu manyan dalilai guda biyu
  • Ya bayyana cewa matsalolin shugabanci da suka dabaibaye NNPP ne suka tilasta masa barin jam’iyyar domin cigaban al’ummarsa
  • Galambi na cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheka zuwa APC, wanda ke kara yawan ‘yan adawa da suka koma jam’iyyar zuwa 11
  • Jam’iyyar NNPP dai ta ta rabu gida biyu, inda wanda suka kafa ta ke takaddama da magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar JigawaJam'iyyar adawa ta NNPP ta sake rasa ɗan majalisar wakilanta, a Hon Yusuf Galambi, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. A ranar Alhamis. Sauya shekarsa na kunshe ne a wata wasika da aka aika wa shugabancin majalisar, Tajudeen Abbas, kuma ya karanta a zauren majalisar yayin zaman da ya gudana a yau.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

Majalisa
Dan jam'iyyar NNPP ya koma APC Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan majalisar na wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa a inuwar jam'iyyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, NNPP.

Sauya shekar na zuwa a daidai lokacin da yan jam'iyyun adawa daga PDP, LP, NNPP da sauransu ke ta koma wa APC bisa dalilai mabanbanta, wanda ya haɗa da rikicin shugabanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisar NNPP ya koma APC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yayin da yake bayyana dalilan sauya shekarsa, Galambi ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan umarnin al’ummar mazabarsa. Haka kuma, ya danganta wannan ci gaba da rikicin shugabanci da ke addabar NNPP, wanda har yanzu an gaza warware wa na tsawon lokaci yanzu.

Hon. Galambi ya ce:

“Wannan ba shawara ta kaina ba ce, umarni ne daga mazabar da nake wakilta,” in ji shi.

NNPP na ci gaba da rasa membobinta

Sauya shekar Galambi ya kawo jimillar ‘yan majalisar jam’iyyun adawa da suka koma APC a cikin watanni shida da suka gabata zuwa kusan 11.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya shiga siyasa a Kano, ya jagoranci magoya bayansa zuwa jam'iyyar APC

Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu, inda a daya bangaren, masu kafa jam’iyyar da aka kora suna ikirarin shugabancinta.

A daya bangaren kuma, magoya bayan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, suna riƙe da shugabancin jam’iyyar, kuma sun ce su IMEC ga sani.

Ɗan takara ya sauya sheka zuwa APC

A wani labarin, mun wallafa cewa Tsohon dan takarar gwamna a jihar Anambra, Valentine Ozigbo, ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ga LP zuwa APC, yana mai cewa ya yi haka ne don ci gaban jiharsa.

Tsohon Shugaban Kamfanin Transcorp ya ajiye mukaminsa a jam’iyyar LP, tare da tsohon sakataren jam’iyyar, Nze Afam Okpalauzuegbu, suka shiga APC a mazabarsu da ke Amesi.

Bashir Ahmad, tsohon hadimin Shugaba Buhari kan sadarwar zamani, ya bayyana sauya shekar Ozigbo a matsayin wata alama da ke nuna rushewar jam’iyyun adawa kafin 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.