Ana Rade Radin Bude Iyakoki, za a Fara Fitar da Abinci daga Arewa zuwa Ketare

Ana Rade Radin Bude Iyakoki, za a Fara Fitar da Abinci daga Arewa zuwa Ketare

  • Gwamnatin Jihar Neja ta fara tattaunawa da hukumar FAAN domin inganta hanyoyin fitar da kayayyakin noma zuwa ketare
  • Hukumar FAAN ta ce za ta hada kai da hukumomi irin su NAFDAC da SON domin tabbatar da tsari mai kyau da zai taimaka wa harkar
  • Rahotanni sun nuna cewa an gabatar da shirin bunkasa ayyukan gine-gine a jihar da suka hada da sunayen tituna da lambar gidaje

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnatin Neja ta fara tattaunawa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) kan samar da hanyoyin da za su inganta fitar da kayan noma daga jihar zuwa ketare.

An gudanar da taron farko ne a ofishin wakilan jihar Neja da ke Abuja, tare da wakilan FAAN da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Amurka ta yi baki biyu, ta musanta zargin dan majalisa kan daukar nauyin Boko Haram

Gwamna Bago
Gwamnatin Neja na shirin fitar da abinci zuwa kasashen ketare. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Neja, Bologi Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar 19 ga Fabrairu, 2025 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FAAN za ta hada kai da hukumomi

Shugaban tawagar FAAN daga filin jirgin saman Abuja, Mista Daniel Tsado Musa, ya ce suna sane da sauyi da ake samu a fannin noma a Jihar Neja.

Ya bayyana cewa hukumar za ta tabbatar da hadin gwiwa da hukumomin da suka dace domin saukaka fitar da kayayyakin noma zuwa kasashen waje.

Mista Tsado Musa ya kara da cewa FAAN za ta samar da hadin kai da hukumomin kamar NAFDAC, SON da NDLEA.

Ya ce za a samar da kayayyakin da suka hada da dakin ajiyar kaya, kariyar tsabar abinci daga cututtuka, tsaro da sauran hanyoyin da za su tabbatar da nasarar shirin.

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Gwamna ya kawo shirin raba abinci kyauta a Ramadan

Gwamnatin Neja na shirye don hadin gwiwa

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, ya ce gwamnatin jihar na shirye don karbar shawarwari daga FAAN da sauran hukumomin da ke da alaka da shirin.

Ya ce za a gudanar da musayar takardu da kuma shirya karin taruka domin fadada hadin gwiwar tsakanin bangarorin.

Kazalika, Shugaban Kamfanin Niger Foods, Mista Sammy Adigun, ya yi bayani kan manyan ayyukan noma da ake gudanarwa a jihar.

Jihar Neja
Yadda gwamna Bago ya samar da kayan noma a jihar Neja. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Ya ce akwai shirin gina yankin sarrafa kayayyakin noma da kuma yankin cinikayya na musamman a filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu da ke Minna.

Za a bunkasa gine-gine a jihar Neja

A yayin taron, wakilin wani kamfanin tsara gine-gine ya gabatar da wani sabon shiri ga gwamnatin Neja.

Shirin ya kunshi samar da sunayen tituna, lambobin gidaje, ginshikan tituna, da kuma shingen rage gudu.

Kara karanta wannan

Haduran tankar mai: Gwamnatin Tinubu ta haramtawa wasu tankoki hawa titunan kasar

Gwamnatin Jihar Neja ta ce za ta duba shirin domin inganta hanyoyin sufuri da kyautata fasalin birane a fadin jihar.

Hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da FAAN da sauran hukumomi na daga cikin matakan da ake dauka domin bunkasa tattalin arzikin Neja.

Za a tura daliban Neja karatu ketare

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Neja na shirin tura daliban jihar karatu kasashen ketare domin karatu mai zurfi.

Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa za a dauki dalibai guda 1,000 daga makarantun gwamnati daga dukkan kananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng