Bayan Tsige Babban Alkalin Jiha, Majalisa Ta Dakatar da Mambobi 13 da Suka Janye

Bayan Tsige Babban Alkalin Jiha, Majalisa Ta Dakatar da Mambobi 13 da Suka Janye

  • Majalisar Dokokin Jihar Benue ta dakatar da ‘yan majalisa 13 da suka nesanta kansu daga tsige alkalin jihar, Mai Shari'a, Maurice Ikpambase
  • Majalisar ta ce dakatarwar ta wata uku an yi ne saboda "rashin da'a” da ka iya haddasa rikici da ɓata sunan majalisar dokoki
  • Kakakin majalisar, Hyacinth Dajoh, ya bayyana sunayen wadanda aka dakatar, inda aka ce wasu sun jefa ƙuri’a sannan suka musanta hakan a bainar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Majalisar Dokokin Jihar Benue ta dakatar da ‘yan majalisa 13 bayan tsige alkalin jihar, Maurice Ikpambase.

An dakatar da yan majalisar ne bayan sun nesanta kansu daga tsige alkalin jihar da aka yi.

An sake dakatar da mambobin Majalisa kan kin amincewa da tsige alkalin jiha
Majalisar jihar Benue ta dakatar da mambobinta guda 13. Hoto: hoto: @BenueHouse (X).
Asali: Twitter

Majalisa jihar Benue ta dakatar da mambobi 13

Bayan zaman majalisa na ranar Talata 18 ga watan Janairun 2025, ‘yan majalisar 13 sun bayyana cewa tsige alkalin ba bisa doka ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

DSS ta gano makamai a ofishin hadimin tsohon shugaban majalisar Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suka ce tsige alkalin ya saba wa dokar raba madafun iko da kuma damar ba da hujja kafin a yanke hukunci a kansa.

A zaman gaggawa da aka yi a yau Laraba, majalisar ta dakatar da ‘yan majalisar 13 na tsawon wata uku saboda "rashin da'a.”

Majalisar ta ce hakan na iya haddasa tashin hankali da ɓata sunan majalisar a idon jama’a.

Ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka kada ƙuri’a don tsige alkalin sun musanta haka a taron manema labarai.

Jerin mambobin da aka dakatar a Benue

Kakakin majalisa, Hyacinth Dajoh, ya bayyana sunayen waɗanda aka dakatar, ciki har da Douglas Akya da Jonathan Agbidye.

Sauran sun hada da Beckie Orpin, Simon Gabo, Williams Ortyom, Onah Blessed, Elias Audu, Anyor Mato da Manger Manger.

Haka kuma akwai Solomon Gyila, Samuel Agada, Abraham Jabi da Ezra Nyiyongo a cikin waɗanda suka samu dakatarwa, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sanata ta riiga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata a ƙasar Amurka

Bayan Tsige alkalin jihar, wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka goyi bayan tsige alkalin sun nesanta kansu daga batun a bainar jama’a.

Shugaban masu rinjaye ya ce hakan ya saba wa dokokin majalisa, don haka suka bukaci a dakatar da ‘yan majalisa 13 na wata uku.

Majalisa ta tsige alkalin jihar Benue

Kun ji cewa Majalisar dokokin Benue ta amince da tsige shugaban alkalan jihar, Maurice Ikpambese, bayan Gwamna Hyacinth Alia ya aike da wasika.

Ana zargin Ikpambese da take dokokin aiki, karkatar da kudaden shari’a, goyon bayan yajin aiki, cin hanci da rashawa, da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.