Dalilan da Yasa Naira Ke Kara Daraja a Shekarar 2025, da Yadda Hakan Zai Daure
A yan kwanakin nan Naira na ci gaba da hawa idan aka kwatanta da dala wanda wasu masana ke ganin na da alaƙa da matakan da bankin CBN ke ɗauka.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban Ƙungiyar ‘yan canji a Najeriya, Aminu Gwadabe ya yi bayanin abubuwan da yake ganin sun taimakawa darajar Naira.
Gwadabe ya bayyana cewa karɓar kuɗin bankuna da CBN ya umarta da sauran dalilai sun ƙarfafa Naira.

Asali: UGC
Masani ya jero dalilan inganta darajar Naira
Nairametrics ta ruwaito cewa naira ta ƙaru da N15 a kasuwar bayan fage cikin mako guda, inda ta rufe kan N1565 kan kowace dala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwadabe ya fadi hakan yayin da yake mayar da martani kan yadda naira ke ƙara ƙarfi a kasuwar musayar kuɗi ta duniya.
“Daga kusan N1660, yanzu muna magana kan N1,552 a kan dala. Wannan babban ci gaba ne.”
“Hanyoyi da dama suna taimakawa, karɓar kuɗin bankuna zuwa BDC kamar yadda CBN ta umarta yana ƙara yawan dala a kasuwa da rage tsoro.”
“Sauran sun haɗa da hutun kasar Sin, wanda ya iya rage buƙatar dala, tsarin 'FX' kuma yana kawo daidaito, da kuma ingantaccen bincike.”
1. Me yasa Naira ke karuwa?
Wasu ba su sani ba, amma Babban Bankin Najeriya (CBN) kwanan nan ya ƙaddamar da sabon tsarin ciniki mai suna 'Enhanced Foreign Exchange Market System' (EFEMS).
EFEMS ya haɗa duk tsofaffin hanyoyin musayar kuɗi na hukuma zuwa tsari guda ɗaya, maimakon rarrabuwa kamar I&E FX Window da sauransu.

2. EFEMS yana tabbatar da gaskiya:
A cewar CBN, EFEMS yana inganta gano farashi da sauƙaƙa ciniki, wanda ke tabbatar da bayyananniyar musayar kuɗi da sauƙin bibiyar kasuwa.
Wannan sauyi yana ba da gudunmuwa wajen haɓaka darajar naira a hukumance, wasu ‘yan kasuwa sun ce yanzu ana samun fiye da buƙatar dala, lamarin da ke ƙarfafa naira.
Sai dai har yanzu ba a san tushe na wadatar dala ba, idan CBN ne ke bayarwa, hakan na iya shafar farashi.
Haka kuma, sabon tsarin ya sa dole a yi ciniki da akalla $100,000, wanda ya dakile wasoson dala, cewar Daily Post.
3. Tsarin yin farashi a kasuwa:
Wani dalili mai yiwuwa shine yadda ake yin oda da farashin musayar kuɗi.
Ba kamar tsohon tsarin da bai bayyana ba, yanzu ana amfani da tsari kamar yadda ake sayar da hannun jari a NGX. Duk waɗanda ke neman saye da sayarwa ana nuna bukatarsu da farashinsu.
Wani jigo a kasuwar ya ce EFEMS yana amfani da tsarin farashin “two-way quote,” wanda ke buƙatar ‘yan kasuwa su nuna farashin da suke son saye da sayarwa.
4. Kasancewar EFEMS sabon tsari ne:
Masana sun ce kasancewar EFEMS sabon tsari na haifar da ƙaƙƙarfan dokoki da bayanan ciniki.
Wani ɗan kasuwa ya ce:
“Saboda sabon tsari ne, mutane na takatsantsan don kada su yi asara.”
Wannan yana taimakawa wajen tabbatar da gaskiya a kasuwa.
Sabbin dokokin bankin CBN sun sa ‘yan kasuwa dole su bayar da rahoton ciniki a cikin mintuna 10 ta hanyar API.
Yan canji kuma na bayar da rahoto ta hanyar tsarin kai tsaye don sauƙaƙa sa ido.

5. Muhimmancin yan canji:
Sabon tsarin ya ba da damar yan canji su sayi dala daga dillalai domin siyarwa ga ‘yan kasuwa.
A baya, ba su da cikakken damar shiga kasuwar FX, amma yanzu suna iya ba da tallafi ga ƙananan ‘yan kasuwa hakan yana hana bambancin farashi sosai tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage.
6. Siyar da dala da gaggawa don tsoron asara:
Wasu ‘yan kasuwa sun ce dalilin hauhawar naira shi ne fargabar masu rike da dala, wanda ya sa suke sayarwa da gaggawa.
Wani ɗan kasuwa ya ce har ya sayar da dala kan N1,500 a kasuwar bayan fage, duk da cewa a kasuwar hukuma farashin ya fi haka.
Rahotanni sun nuna cewa farashin N1,600 ba shi da inganci sosai, kuma gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya tabbatar da hakan.
7. Tashin hankali ga ‘yan kasuwa:
Idan wannan yanayin ya ci gaba, masu ajiyar dala za su iya fuskantar asara, musamman idan farashin ya ci gaba da raguwa.
Wasu sun ce watan Disamba na daga cikin lokutan da naira ke ƙarfafa saboda kudaden da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke turo wa ƙasarsu.
Hakanan, an taba samun irin wannan ƙarfin naira a baya, inda ta tashi zuwa N1,072 a watan Afrilun 2024 kafin ta sake raguwa.
Lokacin nan, CBN ya janye dakatarwar sayar da dala ga yan canji, wanda ya ƙara yawan kudin kasuwa.
Tattaunawar Legit Hausa da masanin tattalin arziki
Lamido Bello ya ce domin inganta Naira dole a kula wurin dakile ayyukan 'Kiripto' da kuma tabbatar da siyan tataccen mai daga matatar Dangote.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya
"Dole ne gwamnati tana siyan taceccen mai daga kamfanin tace mai na Dangote, hakan zai rage bukatar dala domin fita a nemo mai ɗin.
"Dakatar da kamfanin 'Kiripto' musamman Binance wanda zai kara wa Naira karfi a kan dala."
- Lamido Bello
A gefe guda kuma ya ce abubuwan da gwamnati za ta yi wajen tabbatar da dala ta karye tare da dorewar haka sune kamar haka:
"Tallafawa kamfanoni masu sarrafa kayayayyaki da suke amfanar da mutane ta yadda za su iya samun dukkanin sinadaran da suke da bukata cikin sauki ba sai an fita waje ba.
"Gwamnati tasa hannu a duk lokacin da dala ta fara motsi domin kara daidaita farashinta
"Gwamnati ta himmatu wajen samar da abubuwan masarufi da sauran kayayyaki a cikin gida."
- Cewar masanin tattalin arziki
Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Najeriya
A baya, kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya ce da ba a yi amfani da manufofinsa ba, da hauhawar farashin kaya ya iya kai wa 42.81% a Disambar 2024.
CBN ya ce ya ƙara yawan kudaden da 'yan Najeriya ke tura wa daga kasashen waje zuwa $4.18bn cikin watanni uku na farkon 2024.
Asali: Legit.ng