Yadda Sanatoci Suka Jawo Hankalin Tinubu Ya Waiwayi Gyaran Titunan Arewa
A 'yan kwanakin nan, an samu korafe korafe daga yankin Arewacin Najeriya a kan tituna da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kashe N4.2tn wajen gyarawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da sabunta wasu tituna a yankuna daban daban na kasar nan, inda aka ware N4.2tn.
Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje ya yi korafi a zauren majalisar kan cewa Arewa maso Gabas bai samu wakilci yadda ya kamata ba a kudin da aka ware.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin titunan da gwamnatin tarayya za ta gyara da yadda shugabannin yankuna suka yi korafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta gyara
A wani taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da aka gudanar, ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da ware kudi domin gyaran wasu hanyoyi 14.
Daily Trust ta wallafa cewa Ministan ya ce matakin na cikin shirin gwamnatin Tinubu na sake dubi, tsari da kuma fifita manyan ayyukan da aka gada daga gwamnatocin baya.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin hanyoyin da za a gyara akwai titin Kaduna-Jos wanda za a kashe Naira biliyan 33.42.

Asali: Getty Images
Hakanan akwai titin Agaye-Kachia-Baro a jihar Neja da za a kashe Naira biliyan 22 a kansa, da titin Odukpani Junction–Apeti a jihar Kuros Riba wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 26.33.
Sauran titunan sun hada da:
- Titin Abeokuta-Ajibo zuwa Iyana Mosa a jihar Ogun – Naira Biliyan 10.89
- Titin Umuahia-Ikuano-Ikot Ekpene a jihar Abia – Naira Biliyan 14.37
- Titin Yola-Fufore-Gurin a jihar Adamawa – Naira Biliyan 11.81
- Titin Ikorodu-Shagamu a jihar Legas – Naira Biliyan 27.59
- Titin Nkomoro-Isu a jihohin Enugu da Ebonyi – Naira Biliyan 14.49

Kara karanta wannan
"Bai dace gwamnati ta nade hannayenta ba": Ndume ya nemi majalisa ta duba zargi kan USAID
Korafin Sanata Goje ga Shugaba Tinubu
Sanata Danjuma Goje, wanda tsohon gwamnan Jihar Gombe ne, ya nuna damuwa kan yadda yankin Arewa maso Gabas bai samu kaso mai yawa ba a cikin aikin titunan da za a yi.
A cewar Sanata Goje, yankin ya samu ayyuka biyu ne kacal:
- Titin Yola – Fufore – Gurin a Jihar Adamawa
- Titin Karim Lamido a Jihar Taraba
Ya kara da cewa kudin da aka ware domin yin titunan a jimillar kudin bai kai ko kashi daya bisa goma na N4.2tn da aka ware ba.

Asali: Twitter
Danjuma Goje ya lissafo wasu muhimman hanyoyin yankin da ke bukatar gyaran gaggawa, irin su:
- Titin Bauchi – Gombe
- Titin Potiskum – Gombe
- Titin Yola – Mubi
- Titin Biu – Damboa –
- Titin Maiduguri – Numan – Jalingo
Majalisa ta goyi bayan Sanata Goje
Duk da cewa Sanata Goje ne ya gabatar da kudirin, ‘yan majalisa da dama sun nuna goyon bayansu, inda suka bayyana yadda lalacewar hanyoyi ke shafar tattalin arzikin yankin.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su
Sanata Tahir Monguno daga Borno ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas ne yafi kowa fuskantar koma baya a bangaren abubuwan more rayuwa.

Asali: Twitter
Sanata Munguno ya ce rashin wadannan hanyoyi na hana kasuwanci bunkasa, musamman a yankunan da rikicin Boko Haram ya yi wa illa.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa biyo bayan korafin, majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sanya karin tituna a Arewa maso Gabas cikin ayyukan.
Sanata Sani Musa ya yi korafi
Sanata Sani Musa daga Niger ya bukaci a gayyaci Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi bayani kan dalilin da ya sa har yanzu manyan tituna ke lalace duk da kudin SUKUK da ake warewa.
Ya ce yana da muhimmanci a binciki yadda ake tafiyar da kudin gyaran hanyoyi domin gujewa sake fadawa irin wannan matsala a nan gaba.

Asali: Facebook
Sanata Musa ya bayyana cewa kasafin kudin 2025 ya ware Naira tiriliyan 4.3 don ayyukan hanyoyi, amma Jihar Neja ta samu aiki guda daya ne kawai, wato titin Agaie-Katcha-Baro.
Duk da haka Sanata Sani Musa ya wallafa a Facebook cewa titin ma an ware masa kasa da rabin Naira biliyan 1 ne kawai.
A karkashin haka ya ce akwai hanyoyi masu cunkoson jama'a a jihar Neja da suke bukatar kulawar gwamnatin Bola Tinubu wajen sabunta su.
Jingir ya jawo hankalin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce shi ya jawo hankalin gwamnatin Bola Tinubu kan gyara titin Kaduna-Jos.
Malamin ya ce ya jawo hankalin gwamnatin ne da ya gayyaci al'umma ya kafa gidauniyar gyara titin da ya shafe shekaru yana lalace.
Asali: Legit.ng