Ana Fargabar Tsohon Ciyaman Ya Bace bayan Mummunan Harin Yan Bindiga a Kebbi

Ana Fargabar Tsohon Ciyaman Ya Bace bayan Mummunan Harin Yan Bindiga a Kebbi

  • An hasashen batan tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo, Umar Namashaya Diggi a jihar Kebbi
  • Hakan ya biyo bayan harin ‘yan bindiga a kan titin Birnin Kebbi-Diggi wanda ya jefa fargaba a zukatan al'umma
  • Rahotanni sun nuna cewa masu harin sun tilasta masa tsayawa, suka kona motarsa, suka kuma tsere ba tare da an gano inda yake ba
  • Yan sanda sun fara bincike sosai don gano abin da ya faru da Diggi da kuma kamo masu hannu a hari da kuma ɗaukar mataki kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Birnin Kebbi, jihar Kebbi - Ana fargabar batan tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.

An ce Umar Namashaya Diggi, tsohon shugaban Kalgo a jihar Kebbi, ya bace bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kan titin Birnin Kebbi-Diggi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun farmaki maboyar wani babban dan bindiga, an kashe 'yan ta'adda 53

Ana zargin tsohon shugaban karama ya bata a Kebbi
Yan bindiga sun kai hari a Kebbi inda ake zargin batan tsohon ciyaman. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun kai hari a Kebbi

Tribune ta ruwaito cewa an bi Diggi da wata mota da ba san ko na waye ba a kusa da kauyen Gayi da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani majiyar leken asiri ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Fabrairun 2025.

Majiyar ta ce harin yan bindiga ya afku da misalin karfe 12:30 na safiyar jiya Litinin yayin da yake dawowa gida a cikin motarsa.

An zargin tsohon ciyaman ya bace a Kebbi

"Masu harin sun tilasta masa tsayawa, suka kona motarsa kirar Toyota Corolla mai lamba KLG 637 AA, suka tsere, ba a san inda yake ba."

- Cewar majiyar ‘yan sanda.

Rahotanni sun kara da cewa jami'an tsaro sun gano abubuwan da ake zargin an yi amfani da su wajen kai harin da suka hada da kwalba da sanda da mai.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta fara cikakken bincike don gano inda Diggi yake da kuma kama masu aikata laifin, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi magana kan zargin jefawa bayin Allah bam a jihar Katsina

Yan sanda sun ragargaji yan bindiga

Kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kebbi tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun samu nasara kan ƴan bindiga masu ɗauke da makamai.

an sandan tare da ƴan bangan sun hallaka ƴan bindiga mutum huɗu bayan sun sace wani dattijo mai shekara 60 a ƙaramar hukumar Suru.

Jami'an tsaron sun kuma cafke wani ɗan bindiga ɗaya tare da ceto mutumin da aka sace ba tare da ya ji rauni ba yayin harin da aka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.