Gwamnatin Kano Ta Fara Kokarin Kawar da Kungiyoyi Masu Alaka da Ta'addanci a Jihar

Gwamnatin Kano Ta Fara Kokarin Kawar da Kungiyoyi Masu Alaka da Ta'addanci a Jihar

  • Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike kan NGOs bayan an samu kakkarfan zargi a kan wata kungiyar tallafi mai daukar nauyin Boko Haram
  • Da yake kaddamar da kwamitin, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk ya ce za a duba muhimman abubuwa game da kowace kungiya a sassan Kano
  • Ana fatan bibiyar dukkanin muhimman bayanan da za su kore alakar kungiyoyin dake bayar da agaji a Kano da daukar nauyin ta'addanci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin da zai sa ido kan ayyukan kungiyoyin agaji masu zaman kansu (NGOs) da ke aiki a fadin jihar.

Kwamitin, zai mayar da hankali ne a kan binciken hanyoyin da kungiyoyin suke samun kudin da suke gudanar da al'amuransu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙaro rashin imani, sun kashe mutane kusan 20 a garuruwa 2

Jihar
Gwamnatin Kano ta fara bibiyar kungiyoyin dake jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Radio Nigeria ta ruwaito cewa wannan mataki ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi wa wasu kungiyoyin agaji, musamman USAID, da hannu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata ne dan majalisar Amurka, Scott Perry ya zargi hukumar ba da agaji ga kasashen waje (USAID) da daukar nauyin ta'addanci a sassa daban-daban na duniya, ciki har da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Kwamitin Kano zai binciki asalin NGOs

Daily Post ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Faruk, ne ya kafa kwamitin tare da ba shi aikin tantance kungiyoyi agaji na duniya, na kasa, da na cikin gida dake jihar.

Haka kuma, an ba wa kwamitin hakkin binciken tushen kudaden da NGOs ke samu da sauran muhimman bayanai domin kawar da shakku a cikin aikinsu.

Kano na fargaba kan ayyukan NGOs

Wannan mataki ya samo asali ne sakamakon yawaitar damuwa da zarge-zarge kan ayyukan kungiyoyin agaji a jihar, da kuma sabon zargin da ya bulla a kan USAID.

Kara karanta wannan

An kashe shugaban karamar hukuma da magoya bayan APC, PDP suka kacame da fada

Alhaji Umar Faruk ya bayyana cewa kwamitin zai kuma bayar da jagoranci ga kungiyoyin da ke aiki a Kano domin a guda tare, a tsira tare.

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin binciken

Shugaban kwamitin, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fayyace cewa manufar kafa kwamitin ita ce tabbatar da gaskiya da bin doka, ba wai a ci zarafin wata kungiya ko a gallaza mata ba.

A cikin kwamitin akwai manyan jami’ai kamar Alhaji Shehu Abdullahi, mai kula da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) a Kano, da Alhaji Kubarachi, sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA).

Ndume ya shawarci gwamnati kan kungiyoyi

A baya, mun wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayy da majalisar kasar nan da ta tashi tsaye wajen daukar mataki a kan zargin USAID na daukar nauyin ta'addanci.

A wata hira da ya yi, Sanatan ya ce ba wannan ne karon farko da ake samun zargi mai karfi a kan kungiyoyin bayar da agaji wajen daukar nauyin ta'addancin da ke tarwatsa Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.