Dangote Ya Fadi Kalubalen 'Karayar Arziki' da Ya Fuskanta Yayin Gina Matatar Mai
- Aliko Dangote ya bayyana yadda ya fuskanci matsin lamba daga wasu mutane da ke kokarin hana nasarar matatar man fetur dinsa
- Shahararren mai kudin ya ce da aikin matatar ya gaza kammaluwa, da shi kansa ya rasa komai a duniya, kasancewar ya saka jari mai yawa a aikin
- Dangote ya jaddada cewa dole ne Afrika ta fara dogaro da kanta wajen sarrafa albarkatun da take da su maimakon shigo da kayayyaki daga kasashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Hamshakin attajirin Najeriya kuma shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha wajen gina matatar man fetur.
Alhaji Aliki Dangote ya bayyana matsalolin da ya fuskanta daga hukumomi da kuma wasu 'yan kasuwa yayin aikin matatar.

Asali: UGC
A wata hira da ya yi da mujallar Forbes, Dangote ya ce gina matatar man fetur dinsa ce babban taran aradu da ka da ya taba yi a rayuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A karkashin haka, Dangote ya ce da ya gaza kammala matatar da ya shiga cikin mummunan hali maras misaltuwa.
Ya kuma ce daga lokacin da aka fara aikin har zuwa kammalawa, sai da ya sha matsin lamba daga hukumomi, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar mai.
Kalubalen da Dangote ya fuskanta
A cewar Dangote, aikin matatar man fetur da ke da karfin tace ganga 650,000 a kullum ya gamu da cikas iri-iri daga bangarori daban-daban.
Dangote ya ce:
"Na yi gwagwarmaya a rayuwata, kuma har yanzu ban taba gaza cimma burina ba.
"Hatsabiban mutane a harkar man fetur sun fi na miyagun mutane da ke harkar kwayoyi hadari.
"Saboda sukan rikita lissafin mutum, za ka yi wasa da dariya da su, alhali su ne ke maka makirci a bayan fage."
Dangote ya kara da cewa tun farko ya san cewa zai fuskanci matsaloli, amma bai yi tsammanin cewa za su kai haka ba.
Burin Dangote na gina Afrika
Dangote ya bayyana cewa duk da cikas din da ya fuskanta, ba zai taba saduda ba wajen ganin Afrika ta dogara da kanta.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
"Dole mu gina kasashenmu da kanmu, ba wai mu dogara da kasashen waje ba.
"Afrika ba ta da wata matsala sai dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga waje, amma lokaci ya yi da za mu fara sarrafa albarkatunmu da kanmu."
A cewarsa, matatarsa wata babbar dama ce da za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar, tare da kirkirar sababbin hanyoyin habaka arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.
Gwagwarmayar gina matatar Dangote
Dangote ya bayyana cewa aikin matatar man fetur dinsa ne kalubalen da ya fi fuskanta a rayuwarsa, kuma ya dauki tsawon shekaru yana kokarin ganin ya kammala shi.
A cewarsa:
"Wannan shi ne babban hadari da na dauka a rayuwata. Idan da ban yi nasara ba, da ta wa ta kare."
Ya kuma bayyana cewa ya shawo kan matsaloli iri-iri, ciki har da matsin lamba daga hukumomi, wahalar samun kudi da kuma matsalolin shigo da kayayyakin aiki daga ketare.
Dangote ya bayyana cewa yana da shirin sanya matatar tasa a kasuwar hada-hadar hannun jari a cikin shekara daya zuwa biyu masu zuwa.
Haka kuma yana kan shirye-shiryen fadada wasu manyan ayyuka, ciki har da gina bututun iskar gas da zai ratsa teku daga yankin Niger Delta zuwa Lagos.
Dangote ya kuma bayyana cewa yana da burin fadada masana'antar takin zamani da ke karkashin matatar tasa domin habaka tattalin arziki.
Dangote ya fara hada motoci a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa Aliko Dangote ya fara hada motoci a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Dan kasuwar ya bayyana cewa ya fara hada motocin ne da niyyar zama babban mai samar da mota a Najeriya a shekaru masu zuwa.
Asali: Legit.ng