'Ba Shi da Tsoro Ko Kadan': Abin da Tinubu Ya Ce bayan Babban Rashin da Najeriya Ta Yi

'Ba Shi da Tsoro Ko Kadan': Abin da Tinubu Ya Ce bayan Babban Rashin da Najeriya Ta Yi

  • Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar shugaba a kungiyar PANDEF, Cif Edwin Clark a yau Talata
  • Tinubu ya ce Cif Clark ya kasance jagora mai karfin gwiwa wanda ya tsaya kan gaskiya, kuma ya yi gwagwarmaya don adalci da ci gaban yankinsa
  • Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan marigayin da mutanen Neja Delta, yana mai cewa an rasa wani gwarzo mai kishin kasa da hadin kan Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi martani bayan sanar da rasuwar dattijo, Cif Edwin Clark.

Tinubu ya nuna damuwarsa kan rashin marigayi, Clark wanda tsohon kwamishinan tarayya ne kuma shugaba a kungiyar Pan-Niger Delta Forum (PANDEF).

Tinubu ya yi alhinin mutuwar dattijo, Edwin Clark
Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rayawar Cif Edwin Clark. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Dattijo Edwin Clark ya riga mu gidan gaskiya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman (Bayanai da Tsare-tsare), Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Shugabannin Arewa sun yiwa Ganduje kaca kaca, sun kalubalanci tazarcen Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi Cif Clark, mai shekara 97 ya rasu ne a yau Talata 18 ga watan Janairun 2025 bayan fama da jinya.

An haife marigayin a ranar 25 ga Mayun 1927, a garin Kiagbodo, Karamar Hukumar Burutu ta Jihar Delta.

Clark ya yi rayuwa mai cike da tarihi, inda ya yi hidima ga kasa da al'ummarsa a matsayin kansila, kuma mamba a majalisar ministocin jiha da ta tarayya.

Haka kuma, ya kasance mai fafutukar samun iko da albarkatun kasa, adalci na tattalin arziki da na muhalli a yankin Neja Delta.

Tinubu ya jajanta bayan rasuwar Cif Clark

A madadin gwamnatin tarayya, Shugaba Tinubu ya aika da sakon ta'aziyya ga iyalan Edwin Clark, al'ummar Ijaw, mutanen Neja Delta da gwamnatin Jihar Delta.

Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar Cif Clark, yana mai cewa wannan babban rashi ne mai tayar da hankali.

Yayin da yake tunawa da rayuwar marigayi, Shugaban ya ce Cif Clark mutum ne mai tasiri wanda ya yi fice a siyasar Najeriya na tsawon kusan shekaru 60.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje

Shugaban ya bayyana cewa Cif Clark jagora ne mai karfin gwiwa wanda ba ya tsoron fadin gaskiya, ko da zai tsaya shi kadai wajen yaki da zalunci.

Gudunmawar Edwin Clark kan lamuran kasa

''Cif Clark ya tsaya tsayin daka don Neja Delta, ya tsaya don kasa, ra'ayinsa game da al'amuran kasa sun bambanta kuma na kishin kasa.
''Baba Clark, lauya kuma malamin ilimi, ya yi imani da dunkulalliyar Najeriya, kuma har zuwa rasuwarsa, bai dai na kokarin hadin kai ba bisa adalci.
''A matsayin gogaggen dan siyasa, abokan hamayyarsa ba su taba shakkar karfin maganarsa ba, lallai gwarzo ya koma ga Mahalicci.
''Tarihi zai tuna da shi a matsayin wanda ya yi gwagwarmaya don hakkin mutanen Neja Delta, dunkulalliya, da gaskiyar tsarin tarayya.

- Cewar Tinubu

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar samun rahama daga Allah inda ya ta'aziyya ga iyalansa, abokai, da duk wanda wannan babban rashi ya shafa.

Clark ya zargi Ganduje da ta da rigima

Kara karanta wannan

Matawalle ya tsoma baki da Canada ta wulakanta Najeriya, ya fadi matakin da za su dauka

Kun ji cewa dattijo kuma shugaban kungiyar PANDEF ta mutanen Neja Delta, Edwin Clark ya yi martani kan rikicin siyasa a jihar Rivers.

Clark ya zargi shugabannin manyan jam'iyyun APC da PDP da hannu a cikin rikicin domin tozarta Gwamna Siminalayi Fubara Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.