Yan Sanda Sun Ayyana Neman Fitaccen Mawaki Ruwa a Jallo, Sun Gargadi Al'umma
- Rundunar ‘yan sanda a Ogun ta ayyana fitaccen mawaki Habeeb Okikiola a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo
- Rundunar na neman mawaki Portable ne bisa zargin kai hari ga jami’an gwamnati yayin da suke aikinsu a jihar
- An ce Portable da ‘yan daba tara sun kai farmaki tare da makamai, sun ji wa jami’an rauni, amma suka tsere suka kai rahoto wurin ‘yan sanda
- An kama mutum tara amma Portable ya tsere, kuma rundunar ‘yan sanda ta nemi hadin kan jama’a wajen kamo shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Abeokuta, Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ayyana mawaki Habeeb Okikiola a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Mawakin da aka fi sani da Portable ana nemansa ne bisa zargin kai hari kan jami’an gwamnati yayin aikinsu.

Asali: Instagram
Ana neman mawaki Portable ruwa a jallo
Rundunar ta tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a jiya Litinin 17 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar, Omolola Odutola, ta ce a ranar 5 ga Fabrairu, 2025 lamarin ya faru.
Ta ce da misalin karfe 10:00 na safe, jami’an Hukumar Kula da Tsare-tsaren Gini na Ota sun hadu da mahaifin Portable a Odogwu Bar yayin gudanar da aikinsu.
“Bayan sun gabatar da kansu tare da neman takardar izinin gini, mahaifin ya ce musu baya nan, daga baya, Portable da ‘yan daba tara suka kai hari.
Cewar sanarwar
Yadda Portable ya farmaki jami'an gwamnati
Jami’an sun ji raunuka amma suka tsere suka kai rahoto wurin ‘yan sanda, wanda daga baya aka mika maganar ga Sashen Bincike na Manyan Laifuka don daukar mataki.
An kama mutum tara amma Portable ya tsere, kuma an tura gayyata da dama ga Portable amma ya ki bayyana, wanda hakan yasa kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema.
Rundunar ta bukaci jama’a su taimaka wajen ba da bayanai da za su kai ga cafke shi, kuma duk wanda aka samu yana boye shi zai fuskanci hukunci.
Mawaki Portable ya caccaki masu zanga-zanga
Kun ji cewa Mawaki Habeeb Okikiola ya dira kan masu zanga-zanga inda ya ce talauci da rashin aiki ne yake yaudarar matasan da ke son fita.
Mawakin da aka fi sani da Portable ya ce a baya ya fita zanga-zanga amma lokacin ba shi da ko kwabo amma yanzu ya tsira.
Asali: Legit.ng