Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci kan Batun Hana Ƙananan Hukumomin Kano Kuɗinsu

Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci kan Batun Hana Ƙananan Hukumomin Kano Kuɗinsu

  • Babbar kotun Kano ta haramtawa bankin CBN da wasu hukumomin tarayya riƙe kuɗin hananan hukumomin jihar Kano 44
  • Alkalin kotun, mai shari'a Musa Ibrahim Karaye ne ya yanke wannan hukuncin ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025
  • Lauyan ƙananan hukumomin ya ce wannan nasara ta al'ummar Kano ce yayin da APC ta bayyana aniyarta na ɗaukaka ƙara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukunci kan batun riƙe kudaden kananan hukumomi 44 na jihar.

Kotun ta hana gwamnatin tarayya ko wata hukuma ta ƙasa tsoma baki ko riƙe kason kuɗin ƙananan hukumomin jihar Kano.

Abdullahi Abbas da Abba Kabir.
Kotu ta hana hukumomin gwamnatin tarayya riƙe kuɗin kananan hukumomin Kano Hoto: Abdullahi Abbas, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mai shari’a Musa Ibrahim Karaye ne ya yanke wannan hukunci a yau Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025, kamar yadda Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya yi hukunci ne a wata kara da wakilan kananan hukumomi suka shigar domin kare ‘yancin cin gashin kansu na kudi.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun sake yin kuskure, sun hallaka bayin Allah a Katsina

Dalilin shigar ƙarar a Kano

Taƙaddamar da ta kai ga kai ƙara ta samo asali ne bayan jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu ta dakatar da tura kudaden kananan hukumomin Kano.

APC ta yi yunkurin dakatar da tura kudin kai tsaye daga tarayya ne bisa zargin cewa zaben kananan hukumomin da aka gudanar a watan Oktoba 2024 ya saɓa doka.

Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, tare da Hon. Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC, ne suka kai karar hukumomin tarayya da na jiha gaban kotu.

Daga cikin waɗanda suka tuhuma a shari'ar har da babban bankin Najeriya watau CBN, asusun kasafta kuɗaɗen shiga na tarayya (FAAC) da ƙananan hukumomi 44 na Kano.

Babbar kotun Kano ta yi hukunci

Kotun ta yanke hukunci cewa kananan hukumomin na da ‘yancin karbar kudaden su ba tare da katsalandan daga gwamnati ba, rahoton Daily Trust.

Lauyan da ke wakiltar kananan hukumomi, Barista Bashir Wuzirchi, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga Kano.

Kara karanta wannan

Dandazon jama'a sun tarbi Buhari da ya fito zabe na farko bayan gama mulki

"Mun shigar da wannan kara ne domin kare hakkokin Kano daga masu kokarin taɗiye mana ci gaba ta hanyar hana kananan hukumomi kudaden su.
"Alhamdulillah, kotu ta yanke hukunci kuma mu ke da nasara," in ji Wuzirchi.

Jam'iyyar APC za ta ɗaukaka ƙara

Sai dai kakakin APC na Kano, Ahmad Aruwan, ya ce jam’iyyar ba za ta yarda da hukuncin ba, kuma za ta daukaka kara.

"Mu dai burinmu shi ne kare dukiyar jama’a daga hannun shugabanni da ba su cancanta ba. Don haka za mu daukaka kara har sai an yi adalci," in ji shi.

Ƙananan hukumomi: CBN ya zo da sabon tsari

A wani labarin, kun ji cewa batun tura kuɗin kananan hukumomin Najeriya kai tsaye daga asusun tarayya ya gamu da cikas da bankin CBN ya kawo tsare-tsare.

Babban bankin Najeriya ta bukaci kowace karamar hukuma ta gabatar da bayanan yadɗa ta kashe kuɗaɗenta na shekaru biyu kafin buɗe asusu na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262