Gwamna Ya yi Gata ga Talakawa, zai Tura Dalibai 1,000 Karatu Kasashen Waje
- Gwamnatin jihar Neja ta fara tantance dalibai domin samun guraben karatu a kasashen waje a karkashin shirin tallafin Gwamna Umaru Bago
- Shirin zai bai wa dalibai 1,000 daga makarantun gwamnati damar yin karatu a fannonin likitanci, fasaha da noma a Canada, China, India da Brazil
- An riga an gudanar da jarabawar tantancewa a fannonin Turanci, Lissafi, Kimiya, Tarihin Kasa da Ilimin Zamantakewa saura fitar da sakamakon karshe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da shirin tantance daliban da za su samu guraben karatu a kasashen waje a karkashin shirin tallafin gwamna Umaru Bago.
Shirin wanda aka kaddamar domin bai wa daliban da suka yi fice a jarabawarsu dama, zai mayar da hankali ne kan dalibai daga makarantun gwamnati kawai.

Asali: Facebook
Kakakin gwamnan, Ibrahim Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook cewa daliban da za a dauka za su karanci likitanci, injiniyanci, fasahar sadarwa da noma a Canada, China, India da Brazil.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi jarabawar tantance dalibai
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa an riga an gudanar da jarabawar tantancewa domin zakulo daliban da suka cancanta domin samun guraben karatun.
An gudanar da jarabawar ne a fannonin Turanci, Lissafi, Kimiya, Kimiyyar Rayuwa da Ilimin Zamantakewa domin tabbatar da cewa daliban da suka ci jarabawar sun cancanci tallafin.
Gwamnatin ta ce shirin tallafin zai kasance ne bisa cancanta ba tare da nuna bambanci ba, domin bai wa daliban da suka fi hazaka damar cimma burinsu na karatu.
Jami'an gwamnatin sun bayyana cewa shirin yana daya daga cikin manufofin Gwamna Umaru Bago na bunkasa ilimi da samar da damar ci gaba ga matasa.
Maganar kwamishinar Ilimin jihar Neja
Kwamishinar Ilimi ta jihar Neja, Dr Asabe Hadiza Mohammed, ta yaba da kokarin Gwamna Umaru Bago na tabbatar da cewa matasan jihar sun samu damar karatu mai inganci.
Ta ce shirin tallafin zai bai wa matasa damar yin karatu a manyan jami’o’in duniya domin su dawo su tallafa wa cigaban jihar Neja da kasa baki daya.
Haka kuma, Daraktar Gyaran Makarantu da Inganta Ilimi, Hajiya Maimuna Mohammed, ta ce tsarin jarabawar da aka yi wa daliban ya dace da ka’idojin kasa da kasa.
Ta bayyana cewa gwamnati ta dauki matakan tantance daliban da suka fi cancanta domin tabbatar da cewa wadanda suka samu tallafin sun cancanta matuka.
Yaushe za a zabi wadanda suka yi nasara?
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an kammala tantancewa kuma za a fitar da sunayen daliban da suka samu guraben karatun a kasashen waje nan ba da jimawa ba.
Shirin tallafin zai taimaka wajen bunkasa ilimi da samar da karin dama ga matasan jihar da ke da kwazo, ba tare da la’akari da asalinsu ba.
A karshe, an bukaci daliban da suka shiga jarabawar su kasance masu hakuri da jira yayin da ake shirin fitar da sakamakon wadanda suka yi nasara a shirin tallafin.
Gwamna Bago zai karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Neja, Umaru Bago ya dauki matakan samar da tirololin abinci da domin karya farashi a Ramadan.
Gwamna Umaru Bago ya samar da tirololi 1,000, za a sayar da tirela 500 a farashi mai rahusa yayin da za a raba tirela 500 ga mutane marasa galihu kyauta.
Asali: Legit.ng