Abba Ya Dauki Mataki da Ya Ritsa Malaman Kano Sun Sa Dalibai Leburanci
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta wa malamai sanya dalibai yin ayyukan karfi a makarantu, yana mai cewa makaranta wurin koyon ilimi ne, ba wurin wahala ba
- Ya bayar da umarnin dakatar da duk wani aikin da aka sanya dalibai su yi, tare da bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta gyara gine-ginen makarantu da masallatai
- Gwamnan ya duba aikin gyaran wani waje da ya aka lalata yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, inda ya gargadi ma'aikatan su yi aiki cikin gaskiya da rikon amana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi malamai da kada su sanya dalibai yin ayyukan karfi a makarantu.
Gwamnan ya bayyana cewa makaranta wurin karatu ne da koyon tarbiyya, ba wurin tursasa dalibai yin wahalhalu ba.

Kara karanta wannan
Mawaki ya bijirewa mahaifiyarsa, ya koma soyayya da yar majalisa duk da gargadinta

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya ritsa malamai sun saka dalibai aiki
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar bazata zuwa wata makaranta a Kano, inda ya tarar da wasu dalibai suna tono domin gina bayan gida.
Cikin fushi, gwamnan ya tambayi shugabannin makarantar dalilin sanya yara irin wannan aiki mai wahala.
Daily Post ta wallafa cewa shugaban makarantar ya bayyana cewa an ba daliban aikin ne bayan an tashi daga karatu.
Sai dai gwamnan ya haramta irin aiki nan take, yana mai jaddada cewa makaranta ba wurin aikin karfi ba ce.
Abba ya ba da umarnin gyaran makarantu
Bayan haramta wa dalibai yin aiki da karfi, gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta gyara dukkan gine-ginen makarantu da suka lalace.
Haka kuma, ya umarci shugabannin makarantu da su tura duk wani aiki da ke bukatar gyara zuwa ma’aikatar ilimi ko ofishinsa domin a aiwatar.
Ya kuma bada tabbacin cewa za a gyara masallatan da ke cikin makarantun gwamnati domin tabbatar da dalibai sun samu wurin ibada mai kyau.
Gwamnan ya bukaci malamai da su guji amfani da dalibai wajen gyaran makaranta, su bar gwamnati ta dauki nauyin hakan.
Abba ya ziyarci wajen da ake aiki a Kano
Daga nan, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara domin duba aikin gyaran wajen buga takardu na jihar Kano da aka lalata a lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.
Abba Kabir ya nuna damuwa kan yadda wasu gine-gine ba su cika ka’idojin da gwamnati ta gindaya ba, yana mai gargadin 'yan kwangila da ke aikin su cika sharudan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da gina gine-ginen da ba su dace ba, inda ya ce zai sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da ayyukan gyaran.
Abba Kabir Yusuf ya bukaci masu kwangila da su tabbatar da bin dukkan ka’idojin aikin domin kaucewa aikin jeka-na-yi-ka.
Barau ya yi ta'aziyya kan hadarin Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyyar mutanen da suka rasu a hadarin babbar mota a Kano.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi addu'a da wadanda suka rasu da fatan samun lafiya ga wadanda suke kwance a asibiti.
Asali: Legit.ng