Katsina: APC Ta Lallasa Jam'iyyun Adawa a Zaben Ciyamomi da Kansiloli

Katsina: APC Ta Lallasa Jam'iyyun Adawa a Zaben Ciyamomi da Kansiloli

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina (KTSIEC) ta sanar da sakamakon zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi
  • Shugaban hukumar ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da kansiloli
  • Lawal Faskari ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa biyar ne suka fafata a zaɓen wanda aka gudanar da a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2025

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jam'iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Katsina.

Jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 34 da kansiloli 361 a zaɓen wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2025.

APC ta lashe zabe a Katsina
APC ta lashe zaben ciyamomi da kansiloli a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Shugaban hukumar zaɓen jihar Katsina (KTSIEC), Lawal Faskari, ya sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun sake yin kuskure, sun hallaka bayin Allah a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta lashe zaɓe a Katsina

Lawal Faskari ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun da tazara mai nisa.

Shugaban na hukumar KTSIEC ya bayyana cewa an so bayyana sakamakon a ranar Asabar, amma har zuwa dare wasu ƙananan hukumomi 10 ba su kawo na su sakamakon zaɓen ba.

Ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa guda biyar da suka haɗa da AP, BP, AAC, ADC da APC ne suka shiga cikin zaɓen.

Shugaban na hukumar KTSIEC ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, sannan ya yabawa masu kaɗa ƙuri'a kan yadda suka fito zaɓen cikin tsanaki.

IPAC ta yabawa jam'iyyu

A gefe guda, ƙungiyar IPAC reshen jihar Katsina ta yabawa jam'iyyu da suka shiga zaɓen, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da nuna halin zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da shugaban IPAC, Salimu Lawal, da sakataren ƙungiyar, Babangida Kado, suka fitar, sun nuna gamsuwarsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC, ta jawo gagarumar barna

"Ga ƴan takarar mu da suka shiga zaɓen kuma ba su yi nasara ba, muna yabawa da ƙoƙarinku, ƙwazo, da kuma ƙudirinku na son hidimtawa jiharmu."
"Haka zalika, muna yabawa da yadda kuka amince da sakamakon zaɓen da kuma yadda kuke da burin ba da gudunmawarku wajen ci gaban jihar."

- Salimu Lawal

Ɗauki ɗora aka yi

Wani mazaunin garin Kankara, Tasiu Muhammad, ya shaidawa Legit Hausa cewa babu wani zaɓen kirki da aka gudanar.

Ya bayyana cewa ƴan jam'iyyar APC ne kawai suka yi kiɗansu suka yi rawarsu da sunan zaɓe.

"Wannan zaɓen ai dama suna kawai ya tara. Sun yi abin da suke su yi ne kawai amma wannan ba zaɓe ba ne."

- Tasiu Muhammad

Buhari ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Katsina.

Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuri'arsa ne a mahaifarsa ta Daura a zaɓen wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng