Bayan Zargin Masu Hannu a Ta'addanci, Yan Ta'adda Sun Kashe Junansu a Kazamin Hari
- An yi arangama tsakanin Kungiyar Boko Haram tsagin Bakoura da ISWAP a Abadam da ke jihar Borno
- Harin wanda aka kai kan yan kungiyar ISWAP ya yi sanadin kisan manyan kwamandoji da mayaka 31
- An kai harin ne a safiyar Juma'a 14 ga Fabrairun 2025 inda suka yi arangama mai tsanani har zuwa yammaci, suka kwace makamai da kayan aiki./
- Mayakan Boko Haram sun shirya kai hari na gaba kan sansanonin ISWAP a Gemu da Mallam Karamti, yayin da ake sa ran karin arangama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Maiduguri, Borno - Wata mummunar arangama ta barke tsakanin bangarorin ‘yan ta’adda a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.
Mayakan Boko Haram tsagin Bakoura sun kai hari kan ne kan sansanonin kungiyar ISWAP a Abadam.

Asali: Original
An zargi USAID da daukar nauyin ta'addanci
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa an kai harin ne a safiyar Juma'a 14 ga Fabrairun 2025 kan sansanonin ISWAP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan dan majalisar Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da taimaka wa kungiyoyin ta'adda, ciki har da Boko Haram.
Perry ya ce ana kashe $697m a kowace shekara, kuma babu hujjar gina makarantu 120 da aka ce an yi a kasar Pakistan.
Ya kara da cewa kudin da ake ikirarin ana taimaka wa mata, ba su kai gare su ba, sai ma taimaka wa harkar ta'addanci.
An yi arangama da yan ta'adda a Borno
An kai harin ne a Toumbun Gini da Toumbun Ali, inda aka fafata har zuwa yammacin ranar Juma'a.
Majiyoyin sun ce an kashe manyan kwamandojin ISWAP daga ɓangaren Buduma. “Boko Haram ta kashe mayaka sama da 31 na ISWAP."
Cewar wata majiya
Mayakan Boko Haram daga Tsibirin Bokorram sun shirya kai hari kan ISWAP a Gemu da Mallam Karamti, yayin da ake sa ran karin arangama a Kukawa, Daily Post ta ruwaito.
Dan ta'adda ya yi gargadi ga al'umma
A baya, mun ba ku labarin cewa wani da ake zargin kwamandan Boko Haram ne mai suna Mulwuta ya yi barazana ga mazauna Banki a jihar Borno.
Dan ta'addan da ake zargin kwamandan Boko Haram ne ya ce dole mutanen yankin su tuba kafinn watan Ramadan ko a hallaka su.
Barazanar ta haddasa fargaba a yankin, inda jama’a suka shiga damuwa, kasancewar garin ya sha fama da hare-haren ‘yan ta’adda a baya.
Asali: Legit.ng