'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Yi Awon Gaba da Malamin Addini

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Yi Awon Gaba da Malamin Addini

  • Ƴan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Rivers bayan sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika
  • Miyagun ƴan bindigan sun sace Rabaran Livinus Maurice ne tare da wasu mutum biyu lokacin da suke dawowa daga asibiti bayan sun kai ziyara
  • Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce jami'anta na ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da aka sace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a jihar Rivers.

Ƴan bindigan sun sace limamin na cocin Katolika, Rabaran Livinus Maurice ne, tare da wasu mutum biyu.

'Yan bindiga sun sace fasto a Rivers
'Yan bindiga sun sace limamin cocin Katolika a Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Rabaran Livinus Maurice, shi ne limamin cocin St. Patrick’s Catholic da ke Isokpo, a cikin ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace malamin addinin Kirista

Kara karanta wannan

Janar Tsiga: Yadda 'yan bindiga suka shammaci jama'a, suka sace tsohon shugaban NYSC

Malamin addinin an sace shi ne tare da wasu mutum biyu da ba a bayyana sunayensu ba.

Ƴan bindigan sun yi garkuwa da su ne a yayin da suke dawowa daga ziyara a asibiti a kan hanyar Elele-Isiokpo.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin shugaban cocin Katolika ta Port Harcourt, Rabaran Bernadine Anaele, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ƙara da cewa an shigar da rahoton lamarin ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

An kuma buƙaci dukkan mabiya addinin Kirista, musamman na Port Harcourt da Najeriya baki ɗaya, da su ƙara ƙaimi wajen yin addu’a domin a sako limamin da kuma mutanen da ke tare da shi ba tare da wani sharaɗi ba.

Ƴan sanda sun yi magana kan lamarin

Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da cewa rundunar ta samu labarin faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi barna a Gombe, sun hallaka malamin addini

Kakakin ƴan sandan ta ce ƴan sanda sun bazama domin ceto limamin da sauran mutanen da aka sace, kuma za su tabbatar da cafke waɗanda suka aikata laifin.

Ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kebbi sun samu nasara kan miyagun ƴan bindigan da suka addabi mutane.

Ƴan sandan tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun hallaka ƴan bindiga mutum huɗu bayan sun gwabza faɗa.

Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ceto wani dattijo da ƴan bindigan suka yi garkuwa da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng