An Yi Kare Jini Biri Jini tsakanin Boko Haram da ISWAP, Da Dama Sun Mutu

An Yi Kare Jini Biri Jini tsakanin Boko Haram da ISWAP, Da Dama Sun Mutu

  • Rikici mai tsanani ya barke tsakanin bangarorin 'yan ta’addan ISWAP da Boko Haram a kusa da garin Malam Fatori
  • Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa rikicin ya yi sanadin mutuwar 'yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka jikkata
  • Rahotanni na nuni da cewa rikicin yana da nasaba da takaddama kan iko da yankin, wanda ya raunana karfin kungiyoyin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - An samu wani rikici tsakanin 'yan ta’addan ISWAP da na kungiyar Boko Haram masu biyayya ga Bakoura a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Bisa bayanai daga majiyoyin tsaro, rikicin ya faru ne a gabashin Malam Fatori, kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, a yankin gabashin Boso.

Borno
'Yan ta'adda sun gwabza fada da juna a Borno. Hoto: Legit
Asali: Original

Wani jami’in tsaro ya shaida wa Zagazola Makama cewa artabun ya haddasa asarar rayuka masu yawa daga bangarorin biyu, kamar yadda ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Ana shirin kawo karshen zubar da jinin manoma da makiyaya a Jigawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin fadan ISWAP da Boko Haram

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa rikicin tsakanin bangarorin biyu na da nasaba da takaddama kan iko da yankin

Kungiyar ISWAP na kokarin mamaye yankin gaba daya, yayin da mayakan Boko Haram masu biyayya ga Bakoura ke kokarin hana su.

Wani jami’in leken asiri ya bayyana cewa kungiyoyin biyu na fada mai tsanani domin su karfafa tasirinsu a yankin.

An ji cewa rikicisu na baya-bayan nan ya jefa su cikin mawuyacin hali.

A wasu lokuta, irin wadannan rikice-rikice kan kai ga karancin makamai da abinci a tsakanin mayakan kungiyoyin biyu, wanda hakan ke raunana karfinsu.

Asarar rayuka da raunata mayakan ta'adda

Artabun ya haddasa mummunar hasara ga kungiyoyin biyu, inda aka tabbatar da mutuwar mayaka da dama daga kowanne bangare.

Baya ga haka, wasu daga cikin 'yan ta'addan sun samu munanan raunuka sakamakon musayar wuta.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya kai ga bayyanar karin maboyar 'yan ta’addan, wanda hakan na iya taimakawa hukumomin tsaro wajen ci gaba da ragargaza su.

Wata majiya ta ce:

“Daga bayanan da muke da su, mayakan ISWAP da dama sun mutu, haka zalika wasu daga cikin mayakan Boko Haram sun rasa rayukansu.”

Tasirin rikicin ga 'yan ta’adda

Masana harkokin tsaro na ganin cewa wannan rikici zai iya rage karfin kungiyoyin ta’addanci a yankin, kasancewar yawan mayakansu yana raguwa.

Baya ga haka, wannan artabu ya janyo wasu daga cikin 'yan ta’addan sun gudu domin tsira da rayukansu.

A cewar wata majiya, wasu daga cikin mayakan sun gudu zuwa dazukan da ke kusa da iyakar Nijar domin tsira daga rikicin.

Haka zalika, artabun na iya zama wata dama ga jami’an tsaro domin kara fatattakar sauran 'yan ta’addan da suka rage a yankin.

Kara karanta wannan

NNPCL ya shirya hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da jiga jigan Kannywood

Gwamnan Bauchi ya gana da sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bukaci tsaurara matakan tsaro a iyakokin jihar Bauchi yayin da ya gana da sojojin saman Najeriya.

Sanata Bala Mohammed ya bukaci jami'an sojin saman Najeriya su rika sintiri da jiragen yaki a iyakokin Bauchi domin maganin 'yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng