Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar INEC, Ta Jawo Gagarumar Barna
- An samu tashin gobara a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke jihar Sokoto yayin da ake fama da hazo
- Gobarar wacce ta tashi a ofishin hukumar na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta lalata kayayyakin zaɓe masu yawan gaske
- Hukumar INEC ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar wacce ta lalata ginin ofishin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - An samu tashin wata gobara a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke jihar Sokoto.
Gobarar ta tashi ne a ofishin hukumar INEC da ke ƙaramar hukumar Gwadabawa, a jihar Sokoto.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan INEC na ƙasa, Sam Olumekun, ya fitar a shafin X hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC
Gobarar ta lalata aƙalla akwatunan zaɓe 558 da sauran kayayyakin zaɓe.
Sam Olumekun ya bayyana cewa gobarar na iya kasancewa sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi da aka kawo a yankin.
"Gobarar ta tashi da sassafe a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu, 2025, inda ta yi mummunar ɓarna ga dukkan ginin ofishin."
“Kayayyakin da gobarar ta lalata sun haɗa da kujeru da tebura, da kuma kayan zaɓe ciki har da akwatunan zaɓe 558, wuraren kaɗa ƙuri'a 186, jakunkunan zaɓe 186."
"Sauran sun haɗa da tankunan ruwa 12 (masu cin lita 1,000), katifu 400 da bokitai 300."
"Jami'an tsaro da hukumomin kiyaye gobara da suka tura jami'ansu zuwa ofishin na ci gaba da binciken musabbabin tashin gobarar."
"Ba a samu raunuka ko asarar rai ba a yayin tashin gobarar."
- Sam Olumekun
Gobara ta yi ɓarna a ofishin INEC
Ya bayyana cewa gobarar ta yi ɓarna sosai ga ofishin, lamarin da zai iya tasiri a shirye-shiryen zaɓe a yankin.

Kara karanta wannan
"An zuba wa INEC ido ta na sha'aninta," Makusancin Kwankwaso ya dira kan hukumar zabe
Hukumar INEC ta bayyana cewa tana ƙoƙarin duba yiwuwar maye gurbin kayayyakin da suka lalace domin tabbatar da cewa shirye-shiryen gudanar da zaɓe ba su samu cikas ba.
INEC ta dura kan Hudu-Ari
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta dura a kan korarren kwamishinan zaɓenta na jihar Adamawa, Yunusa Hudu-Ari.
Hukumar INEC ta buƙaci korarren kwamishinan da ya je kotu ya kare kansa kan tuhume-tuhumen da ake yi masa na aikata ba daidai ba lokacin zaben 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng