Bayan Shan Suka, daga Karshe an Dage Taron 'Qur'anic Convention' da Aka Shirya a Abuja
Rahotanni sun tabbatar da cewa an ɗage taron 'Qur'anic Convention' da aka shirya yi a Abuja cikin mako biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Taron da za a tara mahaddata Qur'ani sama da 60, 000 ya jawo ka-ce-na-ce dangane da hukuncinsa a musulunci
- An tsara taron ne ranar Asabar, 22 ga Fabrairu, 2025, amma an ɗage shi ba tare da bayyana sabon ranar da za a yi ba
- Wani ɗan kwamitin shirya taron ya tabbatar da ɗagewar, amma dai ba a bayyana musababbin daukar matakin ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar cewa an ɗage taron 'Qur'anic Convention' da aka shirya yi a Abuja a karshen watan Fabrairun 2025.
An dage taron ne wanda ake sa ran zai haɗa mahaddata Qur'ani sama da 60, 000 daga ciki da wajen Najeriya.

Asali: Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Qur'anic Convention': Bala Lau ya nemi hadin kan Musulmi
Rahoton BBC Hausa ya ce an saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron.
Wannan na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau ya ce a shirye suke su karbi gyara kan shirin 'Qur'anic Convention'.
Yayin jawabinsa, Sheikh Bala Lau ya bukaci sauran kungiyoyin Izalah da al'ummar Musulmi su mara wa shirin baya.
An dage taron 'Qur'anic Convention' da aka shirya
An yi fatan taron zai jawo hankalin mahaddata Alkur'ani da dama, amma yanzu an ɗage shi ba tare da bayyana sabon ranar ba.
Wani ɗan kwamitin shirya taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar cewa:
"Tun daren jiya Alhamis 13 ga watan Janairun 2025 aka ɗage yin wannan taro."
Sai dai ba jami'in da ke cikin kwamitin bai bayyana dalilin ɗagewar ko lokacin da za a sake yin taron ba.
Amma kuma majiyar ta tabbatar da cewa ana sa ran bayan watan Ramadan za a iya sanya rana domin gudanar da taron.
Assadussunnah ya shawarci malaman Izalah
A baya, kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yi magana kan rikici tsakanin malaman Izala, ya ce mafi yawan mabiya ba su jin dadi.
Sheikh Asadussunnah ya bukaci malaman Izala su daina kiran juna da sunaye kala kala kamar yadda Alkur’ani ya haramta.
Malamin ya gargadi shugabannin Izala da su mayar da hankali kan matsalolin da suka fi addabar al’umma a kan kokarin kare kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng