Canada Ta Yi Martani kan Rahoton Hana Hafsan Tsaron Najeriya Shiga Kasarta

Canada Ta Yi Martani kan Rahoton Hana Hafsan Tsaron Najeriya Shiga Kasarta

  • Ofishin jakadancin Canada a Najeriya ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa an hana Shugaban Tsaro da wasu jami'ai samun bisa
  • Ofishin ya ce ba zai yi tsokaci kan takamaiman batun neman bisa ba saboda dalilan sirri da tsare-tsare
  • Janar Christopher Musa ya bayyana takaicinsa kan wannan batu, yana mai cewa hakan ya zama dole Najeriya ta tsaya da ƙafafunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan hana hafsan tsaron Najeriya shiga Canada, ofishin jakadancin kasar ta yi magana.

Ofishin ya ce akwai dalilai da ya sanya ta kin fayyace komai game da lamarin da ya shafi Janar Christopher Musa da wasu jami'an sojoji.

Canada ta yi magana kan lamarin hana hafsan tsaro shiga kasarta
Canada ta ce saboda dalilan sirri ba za ta yi magana kan rahoton hana sojojin Najeriya shiga kasar ba. Hoto: HQ Nigerian Army, Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

Ribadu, Janar Musa sun caccaki kasar Canada

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Juma'a 14 ga watan Janairun 2025, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Can ta matse musu': Ribadu ya fusata da aka wulakanta hafsan tsaron Najeriya a ketare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'an sun samu gayyata zuwa wani taro a Canada na girmama jaruman yaki, amma wasu daga cikinsu ba su samu 'visa' ba.

Da yake magana a wani taro a Abuja, Janar Musa ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan batu, yana mai cewa wannan al'amari kira ne ga Najeriya ta tashi tsaye.

“Wannan tunatarwa ce gare mu, mu tsaya kan kafafunmu, mu tsaya da karfinmu a matsayin kasa, mu hana a raina mu.”

- Janar Christopher Musa

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya soki matakin Jakadancin Canada, yana mai cewa wannan abu rashin girmamawa ne ga Najeriya.

Ofishin jakadancin Canada ya yi magana kan lamarin

Ofishin ya tabbatar da samun labarin amma ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda dalilan tsare sirrin bayanai, cewar The Guardian.

"Ofishin jakadancin Canada a Najeriya ya san da rahotannin da ke cewa wasu manyan jami'ai na shirin tafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi bayani a kan daidaita farashin abinci

"Amma saboda dalilan tsare sirri, ba za mu yi tsokaci kan matsayin neman visa na wasu ba.”

- Cewar sanarwar

Ribadu ya gargadi Naja'atu Muhammad kan zarginta

A wani labarin, Mallam Nuhu Ribadu wanda shi ne mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya gargadi Hajiya Naja’atu Muhammad.

Nuhu Ribadu ya bukaci Naja'atu ta janye kalamanta a bidiyon TikTok inda ta zargi Ribadu da goyon bayan gwamnatin Tinubu, wanda a baya ya zargi da cin hanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel