'Ku Bar Sukar Tinubu': Malamin Musulunci kan Tsadar Rayuwa, Ya Kawo Mafita ga Yan Kasa
- Limamin masallacin Abuja, Sheikh Abdulkadir Sholagberu ya yi kira ga 'yan Najeriya su daina zargin Bola Tinubu kan tsadar kayayyaki da wahalhalu
- Malamin ya ce gwamnatin tarayya ta gaji matsalolin tattalin arziki, don haka ya kamata a yi hakuri tare da yin addu’a don ci gaban kasa
- Sholagberu ya bukaci a koma ga Allah, a tuba daga zunubai, tare da neman gafara don Allah ya dawo da komai yadda yake a baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Daya daga cikin sababbin limaman Masallacin Abuja, Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu ya shawarci yan Najeriya.
Malamin ya yi kira ga 'yan kasar su daina zargin Shugaba Bola Tinubu kan tsadar kayayyaki da wahalhalun da ake fuskanta yanzu a kasar.

Asali: Twitter
Halin kunci: Malamin Musulunci ya shawarci 'yan Najeriya

Kara karanta wannan
Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su
Tribune ta ruwaito cewa malamin ya nuna damuwa kwarai kan halin da ake ciki amma ya shawarci yan Najeriya su koma ga Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sholagberu ya ce:
"Maimakon a zargi Shugaba ko gwamnatinsa, ya kamata 'yan Najeriya su koma ga bautar Allah."
Malamin ya bayyana cewa gwamnatin yanzu ta gaji matsalolin tattalin arziki, don haka ya kamata a yi hakuri tare da addu’a don gwamnati ta samu nasarar farfado da tattalin arzikin.
“Dole ne mu koma ga Mahaliccinmu, mu tuba daga zunubanmu, mu nemi gafararsa, domin komai ya dawo kamar yadda yake a baya.”
- Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu
Tsadar rayuwa: Wace shawara malamin ya ba Tinubu?
Sholagberu ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki kwararru a gwamnatinsa wadanda za su taimaka wajen aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma.
Malamin ya yi addu’ar samun nasarar Shugaba Tinubu tare da neman Allah ya ba shi lafiyar jiki da nutsuwa domin cika alkawuran da ya dauka ga al’umma.

Kara karanta wannan
'Can ta matse musu': Ribadu ya fusata da aka wulakanta hafsan tsaron Najeriya a ketare
Haka kuma, ya yi addu’ar zaman lafiya a kasar tare da kira ga ‘yan Najeriya su rungumi hadin kai da zaman lafiya, cewar Vanguard.
Shehu ya gargadi malamai masu sukar juna
A baya, kun ji cewa daya daga cikin limamin masallacin kasa na Abuja, Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu, ya gargadi malamai da masu wa’azi.
Malamin ya bukaci su hada kai inda ya ce sabanin fahimta a addini abu ne da aka saba tsawon lokaci, saboda haka bai kamata ya haddasa gaba ba.
Wannan kira bai rasa nasaba da yawan sukar juna da malamai ke yi musamman bayan shirya taron 'Qur'anic Convention' a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng