Mutane Sun Gaji da Hare Haren 'Yan Bindiga, Sun Fito Zanga Zanga a Zamfara
- Hare-haren ƴan bindiga sun harzuƙa mazauna garin Maru na jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Mutanen garin sun fito kan tituna domin nuna adawarsu kan ƙaruwar hare-hsren ta'addanci da ƴan bindiga suke kai musu
- Zanga-zangar ta jawo an rufe babbar hanyar da ta haɗa Gusau zuwa Sokoto na tsawon awanni kafin sojoji su samu shawo kan lamaarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Mazauna garin Maru na jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zanga kan ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.
Mutanen garin a yayin zanga-zangar sun sun toshe manyan hanyoyi da suka haɗa Gusau da Sokoto domin nuna ɓacin ransu.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka gudanar da zanga-zanga a Zamfara?
An gudanar da zanga-zangar ne kan wani sabon harin da ƴan bindiga suka kai, inda aka sace mutum 32, ciki har da babban limamin garin da iyalansa.
Toshe hanyoyin da aka fara tun ƙarfe 9:00 na safe ya hana zirga-zirgar ababen hawa, inda masu zanga-zangar suka nemi a ɗauki matakin gaggawa don kare rayukan al'umma.
Wani ganau da ya samu kansa a cikin cunkoson motoci na tsawon awanni bakwai, ya bayyana cewa an kawo ƙarshen zanga-zangar ne bayan zuwan dakarun rundunar Operation Fansan Yamma.
Zamfara: Sojoji sun shawo kan mutane
Majiyoyi sun ce shugaban rundunar tsaro da ke kula da ayyukan sojoji a Maru, ya tabbatarwa masu zanga-zangar cewa za a ɗauki matakan ƙara tsaro a yankin.
Tabbacin da ya ba su ne ya sanya suka buɗe hanyar bayan kusan kwashe kusan awanni takwas tana toshe.
Tun daga wannan lokacin na buɗe hanyar, jami’an tsaro sun ci gaba da sintiri a yankin, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan
Katsina: Likitan da ke kula da lafiyar 'yan ta'adda ya shiga hannun jami'an tsaro
Yayin da sojoji ke ci gaba da matsin lamba kan ƴan bindiga, tsageru na ci gaba da kai hare-hare a wurare masu rauni.
Gwamnatin Zamfara ta taɓo batun sulhu da ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta bayyana matsayarta kan yin sulhu da ƴan bindiga.
Gwamnatin ta bayyana cewa babu batun yin sulhu da ƴan bindiga a cikin tsare-tsarenta, domin hakan ba shi ba ne mafita ga matsalar rashin tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng