'Suna Jawo Bala'i': Basarake Ya Haramta Ayyukan Bokaye Mata bayan Kisan Dan Majalisa

'Suna Jawo Bala'i': Basarake Ya Haramta Ayyukan Bokaye Mata bayan Kisan Dan Majalisa

  • Sarki Asagba na Asaba, Epiphany Azinge ya haramta ayyukan bokaye mata da wasu masu asiri, don dakile laifuffuka a yankin
  • An zargi wasu masu bokanci da hannu a kisan dan majalisa na Anambra, wanda aka gano gawarsa a gada bayan sace masa kudi
  • An kuma kafa doka domin tantance mazauna Asaba tare da hana shige da ficen bata-gari a yankin domin ganin an inganta tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Asaba, Delta - Mai Martaba Asagba na Asaba a jihar Delta, Obi Epiphany Azinge SAN, ya haramta ayyukan bokaye mata.

Matakin ya biyo bayan damuwar da aka shiga kan rawar da wadannan kungiyoyi ke takawa wajen tayar da hankula, ciki har da satar mutane da kashe-kashe.

Basarake ya haramta ayyukan bokaye mata a yankinsa
Sarkin Asaba ya dauki mataki kan bokaye mata inda ya haramta ayyukansu saboda kokarin rage laifuffuka. Hoto: Legit.
Asali: Original

Basarake ya fusata kan kisan ɗan Majalisa

Fadar masarautar ta bayyana cewa wannan mataki an dauke shi ne don dakile yawaitar laifuffuka a Asaba da kewayenta, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana fargabar lafiyar mataimakin gwamna da babu labarinsa na tsawon watanni 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta fito ne bayan rahotanni sun danganta masu asiri da wuraren tsafi a Asaba da kisan dan majalisa na Anambra, Justice Azuka, wanda aka gano gawarsa a gada ta Niger.

Da yake magana a taron manema labarai, basaraken ya nuna matukar damuwa kan lamarin, inda ya ce:

“Duk abinda ya faru a wannan kasa zai shafe mu fiye da kowa, ba za mu yarda Asaba ta zama cibiyar miyagun laifuffuka ba.
"Saboda haka, mun dauki matakan gaggawa don dawo da zaman lafiya da tsaro.”

An haramta ayyukan bokaye mata

Sarkin ya jaddada cewa yawancin masu asirin ba 'yan asalin Asaba ba ne kuma sun mamaye yankin da mummunar manufa.

“Muna haramta ayyukan bokaye mata da ba yan asalin Asaba ba kuma ba mu san su ba, ayyukansu, in dai zan fada gaskiya, na bata gari ne.
“Bayan gano alaka da kisan dan majalisar Anambra da masu asiri a Asaba, ya bayyana cewa ba kawai suna taimakawa masu damfara ba ne, har ma suna da hannu a satar mutane, daga yau, an haramta su."

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

- Cewar basaraken

An kuma sanar da cewa duk bokaye a Asaba dole ne su yi rijista tare da bin dokokin majalisar dokoki ta Asaba, Channels TV ta ruwaito.

Basaraken ya ce duk mai gida dole ne ya rubuta bayanan masu haya domin a kowane lokaci mu san su wanene ke zaune a wani wuri.

Basarake ya gargadi kan gulma

Kun ji cewa basarake a jihar Delta, Obi Epiphany Azinge ya gargadi al'umma game da kawo masa gulma musamman a cikin fadarsa.

Mai Martaban da aka naɗa bayan mutuwar tsohon basaraken ya bayyana yadda zai gudanar da mulkinsa a masarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.