'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga bayan Sun Gwabza Fada a Katsina

'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga bayan Sun Gwabza Fada a Katsina

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton wani hari da ƴan bindiga suka kai
  • Ƴan sandan sun daƙile harin ne wanda ƴan bindiga suka kai kan matafiya a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina
  • Bayan an yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ƴan sandan sun yi nasarar korar miyagun ƴan bindigan zuwa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga a jihar Katsina.

Ƴan sandan sun daƙile harin ne wanda ƴan bindiga suka kai a kan titin Yantumaki–Tashan Icce da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a jihar Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan.bindiga sun tafka ta'asa a jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin Katsina

Ƴan sandan sun samu nasarar ceto wasu mutane tare da ƙorar ƴan bindigan bayan an gwabza faɗa.

Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Litinin, inda ƴan bindiga ɗauke da makamai suka tare hanya a kusa da ƙauyen Dorowa, sannan suka buɗe wuta kan motocin da ke wucewa.

A yayin harin, ƴan bindigan sun harbi wata mota ƙirar Ford mai launin ja da kuma Volkswagen Golf, lamarin da ya jikkata fasinjoji biyu.

Ƴan bindigan sun kuma sace wasu daga cikin matafiyan waɗanda ba a bayyana adadinsu ba.

Ƴan sandan jihar Katsina sun kai ɗauki

Bayan samun bayani kan harin sai DPO na ƴan sandan Danmusa ya gaggauta tattara jami’an tsaro na Operation Sharan Daji, inda suka isa wurin harin da lamarin ya auku cikin gaggawa.

Nan take jami’an tsaron suka fafata da ƴan bindigan inda suka yi musayar wuta, wanda hakan ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki 'yan kasuwa a Katsina, sun hallaka bayin Allah

Bayan fatattakar ƴan bindigan, jami'an tsaron sun garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Yantumaki domin samun kulawar likitoci.

A halin yanzu, rundunar ƴan sanda tare da sauran hukumomin tsaro sun tsaurara matakai domin ganin sun ceto mutanen da aka sace ba tare da sun samu wani rauni ba.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne da tsakar rana inda suka tafka ta'asa kan mutanen da ke zaune a cikin ƙauyukan.

A yayin harin, tsagerun sun sace mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da ƙona gidaje da amfanin gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng