Dan Majalisa daga Arewa Ya Fadi Gyaran da Ya Kamata a Yi Wa Kudirin Haraji
- Ɗan majalisar wakilai daga jihar Borno, Ahmed Jaha ya taɓo batun ƙudirin haraji da ke gaban majalisa
- Ahmed Jaha wanda ke wakiltar Gwoza da Damboa ya bayyana cewa akwai sassa daban-daban na ƙudirin waɗanda ke buƙatar a yi musu gyara
- Ɗan majalisar ya nuna adawarsa kan harajin gado da ke cikin ƙudirin, inda ya ce ya saɓawa koyarwar addinan ƙasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar Chibok da Damboa daga jihar Borno, Hon. Ahmed Jaha, ya yi magana kan ƙudirin harajin gwamnatin Bola Tinubu.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya nuna damuwa kan wasu sassa na ƙudirin gyaran harajin saboda akwai wuraren da suke buƙatar a yi musu gyara.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ɗan majalisar ya ce kan ƙudirin haraji?
A cewarsa, tun da farko an nuna damuwa kan ƙuɗirin lokacin da aka gabatar da shi a gaban majalisa saboda yadda ɓangaren zartaswa ya kawo shi.
"Da farko dai, an tura ƙudirin ne duk da ƙin amincewa da shi da majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa ta yi."
"Haka kuma dattawan ƙasar nan sun ƙi amincewa da shi, sannan gwamnonin jihohi, musamman na Arewa, sun nuna rashin amincewarsu kan ƙudirin."
- Hon. Ahmed Jaha
Dalili na biyu a cewar sa shi ne bayan nazari kan ƙudirin, ƴan majalisa sun fahimci cewa akwai wasu sassa da ke buƙatar a sake duba su domin tabbatar da adalci da kyakkyawan shugabanci.
"Wannan ne dalilin da ya sa ƙudirin ya jawo ce-ce-ku-ce tun farko. A wasu lokuta, ƴan majalisa su kan cimma matsaya ɗaya idan buƙatar hakan ta taso, amma a kan wannan ƙudiri, mun samu rarrabuwar kai tun daga farko."
- Hon. Ahmed Jaha
Ɗan majalisa ya hango gyara a ƙudirin haraji
Ya kuma bayyana adawarsa da harajin gado da aka saka a cikin ƙudirin, yana mai cewa hakan ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci, Kiristanci da sauran addinai.
A cewarsa, addinin Musulunci ya yi bayani ƙarara cewa ba a yarda a taɓa dukiyar wanda ya rasu ba.
"Ko a addinin Kiristanci, ko a Musulunci, ko ma a addinin gargajiya, ana kiyayewa tare da kare haƙƙin gadon mamaci."
"Musamman a addinin Musulunci, ba a yarda ko ruwa ka siya daga kuɗin gado ka ba wani wanda ba ya da haƙƙi ko ikon samun wannan gadon."
"Don haka batun cire haraji daga abin da mamaci ya bari ya sabawa koyarwar Musulunci. Kuma ina da yaƙinin cewa hakan ya saba da al’adu da dokokin wasu addinai da dama."
- Hon. Ahmed Jaha
Ɗan majalisa ya soki ƙudirin haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Katsina, Sada Soli ya nuna cewa akwai kura-kurai a cikin ƙudirin haraji.
Ɗan majalisar mai wakiltar Jibia/Kaita ya bayyana cewa an ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu gurguwar shawara kan ƙudirin harajin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng