Gwamna Ya Bankaɗo Ma'aikatan Bogi sama da 2,000, An Shirya Daukar Mataki

Gwamna Ya Bankaɗo Ma'aikatan Bogi sama da 2,000, An Shirya Daukar Mataki

  • Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa an gano kura-kurai a tsarin daukar ma'aikatan da ke aiki da gwamnatin jihar Zamfara
  • Wannan ya biyo bayan rahoton kwamitin da gwamna Dauda Lawal Dare ya kafa domin tsefe ma'aikata kafin biyan mafi karancin albashi
  • Gwamnan ya ce an gano wasu ma'aikatan bogi, da kananan yara da wadanda ya dace a ce sun yi ritaya kuma su na karbar albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta gano ma’aikatan bogi 2,363 bayan kammala tantance ma’aikatan gwamnati da na hukumomin jihar.

Gwamna Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin tantance ma’aikatan jihar a watan Agustan 2024, karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata na jihar, domin gudanar da binciken.

Kara karanta wannan

Ana fargabar lafiyar mataimakin gwamna da babu labarinsa na tsawon watanni 3

Dauda Lawal
Gwamnatin Zamfara ta tantance ma'aikata Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa binciken ya gano yara ƙanana 220 da ke karɓar albashi a matsayin ma’aikatan gwamnati.

Dalilin tantance ma'aikatan gwamnatin Zamfara

Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta jihar Zamfara ta ce tantancewar ta zama dole sakamakon kokarin gwamnati na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Sanarwar ta ce:

"Rahoton karshe da kwamitin ya mika wa Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa an tantance ma'aikata 27,109, yayin da aka gano matsaloli a cikin takardun wasu ma’aikata da suka hada da ma'aikatan bogi 2,363, ma’aikatan da ya kamata su yi ritaya 1,082, ma'aikatan wucin gadi 395, ma’aikata 261 da ba sa cikin jadawalin ma’aikata, 213 da ke kan hutu na karatu, yara ƙanana 220 da ke karɓar albashi, da ma’aikata 67 da aka tura wasu wuraren aiki.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

"Rahoton ya kuma gano cewa ma’aikata 75 sun samu matsala a takardun ɗaukarsu aiki, ba a samu daidaito tsakanin ranar fara aiki da ranar da aka ba su takardar daukar aiki ba, kuma duk su yara ƙanana ne a lokacin da aka dauke su aiki."

An gano ma'aikatan bogi a jihar Zamfara

Gwamnatin Zamfara ta ce bincikenta ya bankado yadda aka cusa sunayen ma’aikatan bogi a cikin jerin masu karɓar albashin gwamnatin jihar.

Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce:

"A yayin tantancewar, an gano ma’aikata bogi 2,363. Wadannan ma’aikata na karɓar jimillar albashin N193,642,097.19 a kowane wata.
"Ma’aikata 1,082 da suka dace su yi ritaya na karɓar jimillar albashin N80,542,298.26 a kowane wata. Haka kuma, an gano ma’aikata biyar da aka tura wasu wuraren aiki suna karɓar N354,927.60 a kowane wata."

Zamfara: Za a dauki mataki kan ma'aikatan bogi

Kwamitin tantance ma’aikatan ya bada shawarar dakatar da ma’aikata 207 da ba su samu tantancewa ba, wanda ake biya jimillar albashi na N16,370,645.90 a kowane wata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta sake fayyace matsayarta kan sulhu da 'yan bindiga

Sanarwar Sulaiman Idris ta ce:

"Kwamitin ya gano ma’aikata 12 da ke cikin jadawalin biyan albashi amma ba sa cikin bayanan gwamnati, inda suke karbar jimillar albashi na N726,594 a kowane wata.
"Wannan tantance wa na daga cikin kokarin da ake yi don tabbatar da ingantaccen aiki da gaskiya a tsarin biyan albashi a jihar Zamfara, musamman duba da fara biyan mafi ƙarancin albashi daga watan Maris na wannan shekara."

Ta'addanci: Gwamnatin Zamfara ta jaddada matsayarta

A baya, kun ji cewa gwamnatin Dauda Lawal Dare ta jihar Zamfara ta ce an yi wa hirar da gwamnan ya yi da ke magana a kan sharudan sulhu da ƴan ta'adda da su ka addabi jihar.

A sanarwar da hadiminsa ya fitar, Gwamna Dauda Lawal ya ce babu abin da zai sa gwamnatinsa ta sassauta wa ƴan bindiga, inda ya ce ana samun nasarar hallaka miyagun mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.