Gwamnatin Kano Ta Yi Rashi, Fitaccen Dan Siyasa Kuma Tsohon Shugaban APC Ya Rasu
- An shiga alhini a Kano bayan rasuwar fitaccen dan siyasa, Ahmadu Haruna Zago, wanda aka fi sani da Ɗanzago, bayan ya sha fama da jinya.
- Rahotanni sun bayyana cewa za a yi jana'izarsa a gidansa da ke Kurna Tudun Bojuwa da misalin karfe 1:00 na ranar yau watau Alhamis
- Kafin rasuwarsa, Ɗanzago ya rike mukamin shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB) a bangaren tsaftar muhalli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar fitaccen dan siyasa a jihar Kano, Ahmadu Haruna Zago.
Marigayin da aka fi sani da Ɗanzago ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya a Kano, kafin rasuwarsa, shi ne shugaban hukumar kwashe shara ta jihar (REMASAB).

Source: Facebook
Lokacin da Abba ya nada Danzago a mukamin

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
Rahoton Leadership Hausa ya ce za a yi jana'izarsa a gidan sa dake Kurna Tudun Bojuwa da misalin karfe 1:00 na rana a fadar Sarkin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada marigayin a mukamin shugaban REMASAB a ranar 5 ga watan Yulin 2023.
Kafin haka, Zago ya kasance jigon APC mai mulkin Najeriya inda ya rike shugabancin tsagi lokacin da ake rikici a jihar Kano.
An sha rigingimu kan kujerarsa ta shugabancin APC yayin da kwamitin uwar jam'iyyar ta sanar da Abadullahi Abbas a matsayin shugaba.
Sai dai Ahmadu Haruna Zago ya kalubalanci matakin inda ya ce an bi ka'ida wurin zabensa a matsayin shugaba.
Abba Kabir ya tura sakon ta'azziya
Yayin da yake ta'aziyya, Gwamna Abba Kabir ya kadu da samun labarin mutuwar Ahmadu Haruna Zago.
Abba Kabir ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook inda ya ce tabbas marigayin jajartacce ne.
Ya ce marigayin ya taka rawa wurin tabbatar da kawo sauyi a siyasar jihar fiye da shekaru 50, ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama.
Al'umma sun yi alhinin rasuwar marigayi Danzago
Mutane da dama sun yi alhinin mutuwar marigayin inda suke yi masa addu'o'i da kuma fatan samun rahama.
Hadimin shugaba Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Abdul'aziz Abdul'aziz shi ma wallafa labarin rasuwar marigayin a shafin Facebook.
A cikin rubutunsa, Abdul'aziz ya ce tabbas marigayin ya sha gwagwarmaya inda ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama.
"Allah ya gafartawa Alhaji Ahmadu Haruna Zago, makaniken jam'iyya, an sha gwagwarmaya."
- Abdul'aziz Abdul'aziz
Legit Hausa ta na sa ran jami'an gwamnatin jihar Kano da manyan mutane za su halarci sallar jana'izar wannan dattijo.
Babu mamaki tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso wanda ya shigo garin Kano da yammacin Laraba ya samu sallar gawar.
Wani tsohon sanata a Kano ya rasu
Kun ji cewa fitaccen dan siyasa a jihar Kano, Sanata Aminu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Marigayin ya rike muƙamin sanata a jamhuriya ta uku karkashin jam'iyyar SDP bayan rasa tikitin takarar gwamna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 79.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

