"An ba Tinubu Gurguwar Shawara," Ɗan Majalisa Ya Tona Kura Kuran da Aka Gano a Kudirin Haraji
- Ɗan majalisar Jibia/Kaita daga jihar Katsina, Hon. Sada Soli Jibia ya ce a farko an ba Shugaba Bola Tinubu gurguwar shawara kan kudirin haraji
- Hon. Sada ya bayyana cewa tun da aka kawo kudirin a farko suka gane cewa waɗanda suka rubuta shi sun yi kura-kurai
- Ya bayyana Tinubu da ɗan siyasa mai wayau, inda ya ce shugaban ƙasar ya bi hanyoyin da ya dace wajen gyara sababbin dokokin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hon. Sada Soli, dan majalisa mai wakiltar mazabar Jibia/Kaita a Majalisar Wakilai, ya ce an ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu gurguwar shawara kan dokokin sauya fasalin haraji.
Ɗan Majalisar ya bayyana hakan ne bayan Majalisar Wakilai ta fara muhawara kan dokokin guda huɗu, wanda shugaban ƙasa ya miƙa mata tun a 2024.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisar Wakilai sun fara tattake wuri kan kudirin harajin Tinubu, bayanai sun fito

Asali: Facebook
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a cikin shirin siyasa a yau ranar Laraba, Sada Soli ya ce kudirin harajin ya nuna ba a ba Tinubu shawara mai kyau ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman jiya Laraba, kudirin sauya fasalin harajin ya tsallaka zuwa karatu na biyu a Majalisar Wakilai ta ƙasa bayan zazzaafar muhawara.
Da yake tsokaci kan abubuwan da aka gano tun farko a dokokin harajin, Sada Soli ya bayyana cewa Arewacin Najeriya ya yi fatali da kudirin dokar ne saboda maslahar kasa baki daya.
Kura-kuran da aka gano a kudirin haraji
A cewarsa ɗan Majalisar, dokokin ba su bi tsarin da ya dace ba saboda ba a tsara su da kyau ba, rahoton Daily Trust.
Hon. Sada ya ce:
“Mu yi wa shugaban kasa adalci. Idan shugaba zai dauki mataki, dole ne ya dogara da shawarar wasu. Ina ganin an ba shi shawara mara kyau.
"Wadanda suka rubuta wadannan kudirori a farko ba su yi aikin yadda ya dace ba, domin a cikin rubutun suna kiran kudirin dokoki (bills) a matsayin dokoki (acts). Wannan ya nuna cewa ba kwararru ne suka tsara dokar ba.”
Shugaba Bola Tinubu ya karbi gyara
Duk da haka, Hon Sada Soli ya ce shugaba Tinubu yana da cikakkiyar fahimta a harkar siyasa kuma yana kokarin tabbatar da adalci a tsarin mulkinsa.
“Tinubu dan siyasa ne mai wayo, yana da tsarin siyasa. Bayan da ya fahimci cewa wadannan dokoki na iya haddasa matsala, sai ya yi nazari sosai.
"Gwamnoni suka duba su, ya umarci Majalisar Dattawa da ta zauna da Antoni Janar na Tarayya, ya kuma tattauna da kakakin majalisa da sauran ‘yan majalisa don a yi cikakken nazari kafin daukar mataki.”
Ɗan Majalisar ya jaddada cewa Shugaba Tinubu yana kokarin tabbatar da cewa an yi shawarwari na gari kafin yanke hukunci kan dokokin gyaran haraji.

Kara karanta wannan
Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA
Majalisa ta tattauna kan kudirin haraji
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta tafka muhawara kan kudirin harajin mai kunshe da sababbin dokoki huɗu a zamanta na ranar Laraba.
Tinubu ya fara yunƙurin gyara fasalin haraji ne bisa shawarwarin kwamitin gyaran dokokin haraji da manufofin kuɗi karkashin jagorancin Taiwo Oyedele.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng