'Yan Bindiga Sun Matsawa Bayin Allah duk da Gwanna Ya Yi Sulhu da Su, Mutane Sun Fusata

'Yan Bindiga Sun Matsawa Bayin Allah duk da Gwanna Ya Yi Sulhu da Su, Mutane Sun Fusata

  • Yayin da gwamnatin Kaduna ke ganin ta fara shawo kan matsalar tsaro bayan sulhu da ƴan bindiga, mutanen Kachia sun koka kan halin da suke ciki
  • Mazauna Ungwan Ate a ƙaramar hukumar Kachia sun fito zanga-zanga, sun ce duk da sulhun da aka yi ƴan bindiga sun hana su zaman lafiya
  • Masu zanga-zangar sun roƙi gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro su kawo masu ɗauki domin tsare rayuka da dukiyoyinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Mazauna Ungwan Ate da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna sun fito tituna a ranar Laraba domin nuna fushinsu kan ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.

Mutanen sun fantsama zanga-zangar ne domin kokawa da jawo hankalin mahukunta kan hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankinsu da kewaye.

Zanga zanga a Kaduna.
Wasu Jama'ar Kaduna sun fito zanga zanga kan ƙaruwar harin yan bindiga Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Zanga-zanga ta barke a kauyen Kaduna

Masu zanga-zangar sun toshe babbar hanyar Ungwan Ate–Ungwan Mission da ke kan titin Kaduna-Kachia, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan binɗiga kofar rago, sun hallaka miyagu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

A cewar wani daga cikin masu zanga-zangar, ‘yan bindiga sun kai hari a Ungwan Ate a daren Talata, inda suka yi sama da sa’o’i biyu suna barnarsu, kuma suka sace mutum guda.

“Ba mu da kariya, wadannan ‘yan bindiga suna kai hari ba tare da wata fargaba ba, kuma ba mu san wa za mu dogara da shi ba.
" Ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa kafin karin rayuka su salwanta,” in ji shi.

Ina sulhun da gwanna ya yi daƴan bindiga?

Masu zanga-zangar sun riƙe kwalaye da rubuce-rubuce kamar:

"Gwamnatin Kaduna ta ce ta sasanta da ‘yan bindiga, amma ana kashe mu kullum a Kachia."
"Mutane da dama na cikin daji suna shan wahala ba tare da sun aikata wani laifi ba."

Kara karanta wannan

Gwamna ya tura manyan motocin buldoza, an rusa fitacciyar kasuwa da tsakar dare

"Ba za mu iya zuwa gona ba, bayan yawancin mu manoma ne ke ciyar da mu."
"Ba mu iya barci da idonmu a rufe. Su wa ke kashe mu?"

Yadda ƴan bindiga suka zafafa hare-hare

Wannan zanga-zanga na zuwa ne yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa a ƙauyukan Kachia da suka haɗa da Gadanji, Ungwan Wage, Ungwan Alhaji, Agunu Dutse, Maro, da Ungwan Dauje.

Al’ummar yankin sun koka da cewa babu wadataccen tsaro duk da yawan koke-koken da suka aika wa hukumomi, rahoton Daily Post.

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bai samu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A halin yanzu, mazauna yankin na cigaba da rokon gwamnati da ta gaggauta daukar matakin dawo da zaman lafiya a yankin.

Yan bindiga sun kashe mutum 2

Kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki wasu kauyuka a yankin karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna, sun kashe mutum biyu.

Maharan, waɗanda suka shiga cikin garuruwan da yawansu, sun buɗe wuta ba kakkautawa a harin, lamarin da ya jefa jama’a cikin tashin hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: