Manyan Sarakuna 5 Masu Daraja da Kotu Ta Tsige daga Sarauta a cikin Shekara 1

Manyan Sarakuna 5 Masu Daraja da Kotu Ta Tsige daga Sarauta a cikin Shekara 1

  • Sarakuna a Najeriya na da tasiri sosai a cikin al’umma, amma abubuwan da suka faru kwanan nan sun sa wasu ‘yan kasa fara shakkun ƙarfinsu
  • A yanzu ɗai makomar sarakuna na kara komawa hannun ƴan siyasa da kotuna, a shekara guda da ta gabata akalla masu martaba biyar suka rasa sarautarsu
  • Misali na baya-bayan nan shi ne sauke Ohinoyi na Ebiraland, Mai Martaba Alhaji Ahmed Muhammed Tijani Anaje wanda kotu ta warware rawaninsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - A ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu, wata babbar kotu a jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta tsige Ohinoyi na Ebira, Ahmed Tijani Anaje.

Mai shari’a Salisu Umar, alkalin babbar kotu ta shida da ke Lokoja, ne ya yanke hukunci, ya umurci wanda ake kara da ya daina gabatar da kansa a matsayin sarkin ƙasar Ebira.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Sarkin Ebiraland.
Sarkin Ebiraland, Mai Martaba Ahmed Tijani Anaje wanda kotu ta tuɓewa rawani a jihar Kogi Hoto: @a_yellows
Asali: Twitter

Sarakunan Najeriya da kotu suka tsige kwanan nan

Rahoton Vanguard ya ce karar da ta kai ga tsige Ohinoyi na Ebira, Ahmed Tijani Anaje, ta samo asali ne daga korafin da mutane uku suka shigar, suka kalubalanci sahihancin nadinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa an samu kura-kurai a tsarin da aka bi wajen naɗa shi a matsayin Ohinoyi na Ebiraland.

Ahmed Anaje ya hau karagar sarauta ne da tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya naɗa shi a watan Janairu na shekarar 2024.

Dangane da wannan ci gaban da ya faru a jihar Kogi, Legit Hausa ta duba wasu manyan sarakuna biyar da kotuna suka tsige daga kujerunsu tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.

1. Sarkin Ebira a jihar Kogi (Ohinoyi na Ebiraland)

A ranar 3 ga Fabrairu, 2025, wata babbar kotu da ke Lokoja a jihar Kogi, ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tijani Anaje daga sarautar Ohinoyi na Ebiraland.

Kara karanta wannan

"An ba Tinubu gurguwar shawara," Ɗan Majalisa ya tona kura kuran da aka gano a ƙudirin haraji

Mai shari’a Salisu Umar ya umarce shi da ya daina bayyana kansa a matsayin sarkin ƙasar Ebira, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Sarkin Ebira.
Kotu ta tsige sarkin kasar Ebira, Ahamd Anaje Hoto: Ebiraland
Asali: Facebook

Dr. Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu ne suka shigar da karar bisa zargin rashin bin ka’ida a lokacin da aka nada shi a watan Janairu 2024.

2. Alexander Macgregor (Olu na Ilawo)

A ranar 28 ga Janairu, 2025, wata babbar kotun jihar Ogun mai zama a Abeokuta ta soke nadin Alexander Macgregor a matsayin Olu na Ilawo.

Kotun ta bayyana tsarin da aka bi wajen naɗin basaraken a matsayin wanda ya saɓa doka da ka’idar masarauta.

Alexander Macgregor.
Kotu ta tsige Alexander Macgregor (Olu na Ilawo) daga sarauta Hoto: Akinlawon Hademola
Asali: Facebook

Mai shari’a Olatokunbo Majekodunmi ya umarce shi da ya daina gabatar da kansa a matsayin Olu na Orile Ilawo har sai an kammala sauraron karar da ke gabansa.

Punch ta ruwaito cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne a shari'ar da ƴan gudan sarautar Ogunsanya suka shigar, suna neman a sauke sarkin daga mulki.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

3. Oba Olatunji Kalejaiye (Nloku na Iraye)

A watan Nuwamba 2024, Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da sauke Oba Olatunji Kalejaiye daga sarautar Nloku na Iraye a karamar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun.

Hukuncin ya tabbatar da na kotun daukaka kara da ya umarce shi da ya daina gabatar da kansa a matsayin Nloku na Iraye, kamar yadda The Nation ta kawo.

Kotun koli.
Kotun koli ta tsige sarki a jihar Ogun, Oba Olatunji Kalejaiye Hoto: Supreme Court of Nigeria
Asali: Twitter

4. Oba Femi Olugbesoye (Oluloro na Iloro Ekiti)

A watan Oktoba 2024, babbar kotu a Ado Ekiti ta tsige Oba Femi Olugbesoye daga sarautar Oluloro na Iloro Ekiti bisa zargin rashin bin al’ada da ka’idojin gargajiya wajen nadinsa.

Mai shari’a Jide Aladejana ya yanke hukuncin ne a karar da wasu ‘ya’yan gidan sarauta suka shigar suna kalubalantar nadin basaraken.

Oba Femi Olugbesoye.
Kotu ta sauke basarake daga kan sarauta a jihar Ekiti Hoto: Oba Femi Olugbesoye
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce tun kafin nan dai mutanen yankin sun yi zanga-zanga kan naɗin sarkin, suka buƙaci gwamnatin Ekiti ya tube masa rawani ta naɗa wanda suka fi so.

Kara karanta wannan

Shirin ƙarin kuɗin kira da sayen data a Najeriya ya gamu da cikas, Majalisa ta tsoma baki

5. Oba Johnson Ajiboye (Olola na Ola)

A watan Afrilu 2024, Mai shari’a Lawrence Arojo na babbar kotun jihar Osun ya sauke Oba Johnson Ajiboye daga sarautar Olola na Ola a karamar hukumar Ejigbo.

Hukuncin babbar kotun dai ya rushe naɗin da Gwamna Ademola Adeleke ya yi wa sarkin a jihar Osun.

Gwamna Ademola Adeleke.
Kotun jihar Osun ta rushe naɗin sarkin da Gwamna Adeleke ya yi Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Bayan hukuncin, wasu masu adawa da shi sun gargade shi da ya daina gabatar da kansa a matsayin Olola na Ola, kamar yadda Punch ta tattaro.

Naɗa Sarki ya bar baya da ƙura a Oyo

A wani labarin, kun ji cewa Yarima Ismaila Olamilekan Owoade ya maka Gwamna Seyi Makinde a kotu, yana kalubalantar naɗin sabon Alaafin.

Mai ƙara ya maka gwamna da wasu mutum 19 a gaban kotun Oyo, inda ya shaidawa alkali cewa an nada Prince Abimbola Owoade ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262