Ba kanta: An Nemi Bindigogi 3,907 An Rasa a Ofisoshin 'Yan Sandan Najeriya

Ba kanta: An Nemi Bindigogi 3,907 An Rasa a Ofisoshin 'Yan Sandan Najeriya

  • Majalisar dattawa ta titsiye sufeto janar kan bacewar bindigogi 178,459, ciki har da AK-47 guda 88,078 a ofisoshin rundunar 'yan sanda
  • Sanata Onyekachi Nwebonyi ya ce bacewar makaman na taimakawa wajen matsalar tsaro a kasar, kuma "jama'a na hakkin sanin inda suke"
  • Rahoton akanta janar ya nuna makaman da aka saya da kudin harajin jama’a sun yi batan dabo, lamarin da jawo damuwa kan tsaron kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin jama’a na majalisar dattawa ya titsiye sufeto-janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a kan rahoton bacewar bindigogi 178,459.

Sufeto janar na 'yan sanda ya samu wakilcin mataimakin sufeto janar mai kula da asusu da kasafin kudi, Abdul Sulaiman, a zaman majalisar na ranar Talata.

Majalisar dattawa ta titsiye 'yan sanda kan batan bindigogi 3,907
An gano bindigogi 3,907 sun bace daga ofisoshin 'yan sanda, majalisa ta fara bincike. Hoto: @FCT_PoliceNG, @NGRSenate
Source: Twitter

Bindigogi 3,907 sun bace daga hannun 'yan sanda

Rahoton binciken 2019 na akanta janar na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira, ya ce mafi yawan bindigogin da suka bace kirar AK-47 ne, inji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa ya fito ya faɗi gaskiya, ya bayyana kuɗin da aka tura wa ƴan bindiga

Daga cikin bindigogin da ba a iya gano inda suke ba, guda 88,078 kirar AK-47 ne, yayin da sauran su suka kasance bindigogi iri daban-daban.

Rahoton ya kuma bayyana cewa har zuwa watan Janairun 2020, bindigogi 3,907 sun bace daga ofisoshi daban-daban na ‘yan sanda a kasar nan.

Sufeta janar ya gurfana gaban majalisar dattawa

Majalisar Dattawa ta kira sufeto-janar din da ya gurfana a gabanta ko kuma ya fuskanci kamu, lamarin da ya sa ya aiko wakilinsa domin sun yi bayani.

AIG Suleiman ya wakilci Egbetokun, inda ya bayyana cewa rashin zuwan shugaban 'yan sandan a baya ba alamar raini ba ne ga majalisar.

Daga cikin tambayoyin bincike da aka yi wa rundunar, akwai batun raba kwangiloli na sama da Naira biliyan daya ba bisa ka'ida ba.

Majalisa ta nuna damuwa kan bacewar makaman

The Nation ta rahoto cewa, abin da ya fi jawo hankali a zaman shi ne bacewar bindigogi, musamman daruruwan bindigar AK-47, a ofisoshin ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

'Najeriya ta rasa aboki': An shiga jimami da tsohon shugaban kasa ya kwanta dama

Shugaban riko na kwamitin, Sanata Onyekachi Nwebonyi, ya nuna damuwarsa game da rahoton, yana cewa lamarin na taimakawa wajen tabarbarewar tsaro.

“Aikin gyaran tsaro ba zai yiwu ba idan makamai suna yawo a hannun wadanda ba su dace ba,” inji Sanata Nwebonyi.

Dan majalisar dattawan ya kara da cewa wannan lamarin ya saba wa bukatar gwamnati na inganta tsaro a Najeriya.

Majalisa ta nemi a gano inda bindigogin suke

Sanata Nwebonyi ya kara da cewa:

“Idan har wadannan bindigogi suna hannun ‘yan ta’adda, babu wanda ke cikin aminci, hatta ku kanku ‘yan sanda ba ku tsira ba."

Mukaddashin shugaban kwamitin ya bukaci a bincika lamarin sosai domin bayyana inda makaman suka tafi da kuma dalilin bacewarsu.

"Makaman nan an saye su ne da kudin harajin ‘yan Najeriya, don haka suna da hakkin sanin inda suka tafi."

- Sanata Nwebonyi.

Kwamitin ya nemi a fitar da cikakken rahoto kan bacewar bindigogin tare da daukar matakin da ya dace domin tabbatar da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com