Jami'in Binance da Aka Tsare Ya Fadi Yadda Abba Kyari Ya Taimake Shi a Gidan Yari

Jami'in Binance da Aka Tsare Ya Fadi Yadda Abba Kyari Ya Taimake Shi a Gidan Yari

  • Wani babban jami'i a kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, ya bayyana yadda Abba Kyari ya taimaka masa a gidan gyaran hali na Kuje
  • A Kuje, Gambaryan ya kasance a sashen manyan mutane (VIP) tare da manyan fursunoni, ya samu kulawa ta musamman daga Abba Kyari
  • Bayan shan wahala a tsare, Gambaryan ya samu ‘yanci da EFCC ta janye tuhumar da ta ke yi masa, amma ya ce yana so ya samu adalci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jami'in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan da aka zarga da zambar kudi da ciniki da kudin kasashen waje, ya bayyana wahalar da ya sha a tsare.

Gambaryan ya yaba wa tsohon mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari kan irin gudunmawar da ya ba shi yayin da yake kulle.

Kara karanta wannan

"Dalilina na sukar BolaTinubu a baya," Hadimin shugaban kasa

Jami'in Binance ya yaba wa Abba Kyari kan tiamakonsa a gidan kaso
Jami'in Binance da ake tuhuma kan zargin cin hanci ya yaba wa Abba Kyari. Hoto: Abba Kyari, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

Jami'in Binance ya yabawa Kyari a gidan kaso

A wata hira da yayi da Wired wanda The Guardian ta bibiya, Gambaryan ya bada labarin yadda tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sandan ya taimaka masa a gidan yarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gidan yarin Kuje, an sanya shi a sashen manyan mutane, aka ba shi daki mai girma da gadaje na karfe, da karamin taga mai sanduna.

“Duk da haka, hakan ya fi dakin EFCC, domin ina samun hasken rana da iska daga waje."
“Kyari shi ne Red dina, ina kwatanta shi da Morgan Freeman a fim din The Shawshank Redemption, shi ne ya taimaka mani a rayuwa.”

- Cewar Gambaryan

'Yadda Abba Kyari yake da tasiri a gidan kaso'

A sashen VIP, Gambaryan ya hadu da sanannun fursunoni, ciki har da dan uwan mataimakin shugaban kasa da kuma wani da ake shirin mikawa Amurka.

Ya ce Kyari yana da iko sosai a gidan yari, inda ma’aikata da fursunoni ke mutunta shi, kuma matarsa tana kawo abinci ga dukkan su.

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Gambaryan ya ce yana son wani abinci na Arewa da matar Kyari ke yi, don haka tana dafa masa.

Sai dai, Gambaryan ya jaddada cewa bai taba biyan kudin cin hanci ba, duk da cewa jami'an gidan yari na bukatar makudan kudi daga wasu fursunoni.

Kotu ta tura keyar jami'in Binance kurkuku

A baya, kun ji cewa Kotun Tarayya ta zauna domin cigaba da shari'ar jami'in kamfanin Binance bisa zargin ketare biyan haraji da ake yi masa.

Alkalin kotun, Mai shari'a Emeka Nwite ya ki amincewa da neman belin Tigran Gambaryan da lauyansa ya yi kan rashin lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.