Safarar Kudi: Jami’in Binance Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Kotu, Alkali Ya Dauki Mataki

Safarar Kudi: Jami’in Binance Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Kotu, Alkali Ya Dauki Mataki

  • Jami'in Binance, Tigran Gambaryan, ya yanke jiki ya fadi a gaban kotun a lokacin da aka gurfanar da shi a jiya Alhamis
  • Lauyan Gambaryan, Mark Mordi, ya ce shaidawa alkali cewa wanda ya ke karewa ba shi da lafiya kuma an aikawa kotu da takarda
  • A baya mun ruwaito babbar kotun tarayyar ta ki ba da belin Gambaryan saboda fargabar zai iya tserewa idan har ya samu sarari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An samu wata 'yar takaddama a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis lokacin da jami'in Binance, Tigran Gambaryan, ya yanke jiki ya fadi a gaban kotun.

Gambaryan, wanda ke zaune a kujerar baya a cikin kotun, bai gurfana a gaban alkalin kai tsaye a lokacin da magatakarda kotun ya kira shari'ar ba.

Kara karanta wannan

Shaye shaye: Mahaifi ya bukaci kotu ta daure dansa a jihar Kano

An gurfanar da jami'in Binance a kotu
Jami'in Binance ya yanke jiki ya fadi a gaban kotu. Hoto: officialefcc
Asali: Facebook

Daga baya ne ya mike tare da tunkarar alkalin bayan da Emeka Nwite, shugaban alkalan kotun ya tambayi inda wanda ake kara (Gambaryan) na 2 yake, in ji rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in Binance ya yanke jiki ya fadi

Daya daga cikin lauyoyin masu kare wadanda ake kara ne ya taimaka wa babban jami'in na Binance yayin da yake tafiya zuwa gaban kotun.

Sai dai kafin ya karasa Tigran Gambaryan ya yanke jiki ya fadi. Daga baya aka sake taimaka masa ya daddafa zuwa kujerun gaba ya zauna.

Jaridar The Punch ta ruwaito lauyan Gambaryan, Mark Mordi, ya ce wanda yake karewa ba shi da lafiya kuma an aika da takarda domin sanar da kotu halin da yake ciki.

"Ya mai girma mai shari'a, hakika ba lallai ne a gudanar da wannan shari'ar a yau ba."

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

- Mark Mordi

Kotu ta hana belin jami'in Binance

Tun da fari, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayyar ta ki ba da belin jami'in Binance, Tigran Gambaryan saboda fargabar zai iya tserewa idan har ya samu sarari.

Kotun ta ki bayar da belin ne watanni biyu bayan Nadeem Anjarwalla, wani jami'in na Binance ya tsere daga hannun ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) na Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.