Nnamdi Kanu Ya Tayar da Kura a Kotu, Ya Nuna Tirjiya a gaban Alkali

Nnamdi Kanu Ya Tayar da Kura a Kotu, Ya Nuna Tirjiya a gaban Alkali

  • Alkaliyar babbar kotun tarayya, Mai shari'a Binta Nyako, ta dage shari’ar Nnamdi Kanu ba tare da tsayar da ranar cigaba ba
  • A yayin zaman kotun, Nnamdi Kanu ya nuna cewa bai yarda da alkalancin Nyako ba, saboda ta riga ta janye kanta daga shari’ar
  • Lauyan masu shigar da kara ya bukaci a sa rana domin ci gaba da shari’a, amma alkalin ta dage shari’ar ba tare da tantama ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, ba tare da tsayar da rana ba.

Wannan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Kanu da alkalin kotun, Binta Nyako, inda ya bayyana cewa bai yarda ta ci gaba da sauraron shari’arsa ba.

Kara karanta wannan

"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki

Nnamdi Kanu
Kotun tarayya ta daga shari'ar Kanu. Hoto: Kola Sulaimon
Source: Twitter

Rahoton da jaridar The Cable ta wallafa ya nuna cewa an dawo da shari’ar ne gaban Nyako, bayan da babbar kotun tarayya ta ki amincewa da janyewarta daga sauraron karar.

Kanu, wanda ake tuhuma da aikata ta'addanci, ya bayyana a gaban kotu, ya sake kalubalantar hurumin alkaliyar a shari’ar tasa.

Rikici tsakanin Nnamdi Kanu da Binta Nyako

A zaman kotun da aka yi a ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu, Kanu ya yi tir da sake dawo da shari’arsa gaban Binta Nyako, yana mai cewa ba ta da hurumin ci gaba da sauraron shari’ar.

Tun a watan Satumba na shekarar 2024, Kanu ya nemi alkalin ta janye daga sauraron shari’arsa, yana mai cewa ba shi da kwarin gwiwa kan adalcin da za ta yi.

Duk da haka, babban alkalin kotun tarayya, John Tsoho, ya mayar da karar ga Nyako, yana mai cewa dole ne a gabatar da bukatar janyewar a rubuce.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An maka Shugaba Tinubu a kotu kan badakalar kwangilar Naira biliyan 167

Lauyoyin bangarori sun yi tirjiya a kotu

A wani kokari na ci gaba da shari’ar, lauyan masu kara, Adegboyega Awomolo, ya bukaci kotu da ta tsayar da rana domin ci gaba da sauraron karar, yana mai cewa shaidunsu sun shirya tsaf.

Sai dai lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya bayyana a cikin wata wasika da ya aika a ranar 9 ga watan Disamba, cewa janye hannu da Binta Nyako ta yi daga shari’ar yana nan daram.

Kanu ya bukaci a mayar da shari’ar zuwa kotun tarayya da ke yankin Kudu maso Gabas, amma wannan bukata ba ta samu karbuwa ba.

Nnamdi Kanu ya caccaki hurumin kotu

Kanu ya bayyana fushinsa kan yadda aka dawo da shari’arsa gaban Binta Nyako, yana mai cewa bai yarda da ikon kotun a kansa ba.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Nnamdi Kanu ya bayyana cewa duk abubuwan da alkalin ta fada ba su da ma’ana a gare shi.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya tabbatar da korar Kwankwaso da Buba Galadima a jam'iyya

Ya ce yana halartar kotu ne kawai don girmama dokokin kasa, amma a ganinsa ba ya bukatar kotun Nyako ta saurare shi.

Kanu ya ce rashin sanin ilimin doka na mayar da Najeriya baya yayin da ya zargi kotun da karya dokokin kasa.

Gwamnoni sun yi taro a kan Nnamdi Kanu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Kudu maso Gabas sun yi taro na musamman kan halin da Nnamdi Kanu ke ciki.

An ruwaito cewa gwamnonin za su bukaci gwamnatin tarayya ta saki Kanu da ake zargi da laifuffuka da suka shafi ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng