"Muna da Hujjoji," Jigon APC Ya Cire Kunya, Ya Karyata Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari

"Muna da Hujjoji," Jigon APC Ya Cire Kunya, Ya Karyata Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari

  • An fara caccakar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kan ikirarin da ya yi cewa ya inganta tsaro da tattalin arziki a lokacin da yake ofis
  • Jigon APC mai mulki, Josef Onoh ya ce abin da Buhari ya faɗi ba gaskiya ba ne domin komai lalacewa ya yi a mulkinsa na shekaru takwas
  • Mista Onoh ya ce dubannin mutane sun rasa rayukansu a mulkin Buhari, sannan tattalin arziki ya ƙara taɓarɓarewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jigon APC, Josef Onoh, ya ce mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas cike yake da cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tsaro.

Mistah Onoh ya ƙaryata ikirarin da Buhari ya yi cewa gwamnatinsa ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya kuma ta inganta tsaro a shekaru takwas.

Muhammadu Buhari.
Jigon APC ya musanta ikirarin Buhari, ya ce gazawarsa a shekaru takwas ce take wahal da gwamnatin Tinubu Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Josef Onoh ya fadi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumma’a a matsayin martani ga kalaman tsohon shugaban ƙasa Buhari, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Tun farko Buhari ya ce ya gaji tattalin arziki mai rauni da matsalolin tsaro daga Jam’iyyar PDP, wacce ta shafe shekaru 16 tana mulkin kasar nan kafin ya karɓa a 2015.

Buhari ya yabi kansa, yana mai cewa tattaunawa da dabarun gwamnatinsa sun taimaka wajen rage matsalar ta’addanci da koma bayan tattalin arziki.

Martanin Onoh kan ikirarin Buhari

Da yake mayar da martani kan wannan ikirari, Onoh ya ce tattalin arzikin Najeriya ya rushe, cin hanci da rashawa sun yi katutu, kuma matsalar tsaro ta kara tabarbarewa a lokacin mulkin Buhari.

Ya kara da cewa ko a yanzu gwamnatin Bola Tinubu na fama da wahala ne sakamakon gazawar Buhari wajen tafiyar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

Jigon APC ya ce:

“A yau, ‘yan Najeriya na cewa gwamnatin Tinubu ce mafi muni da suka taba gani, ba tare da sun fahimci cewa shugaban ya yi shiru ne kawai yana ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansa ba tare da korafi ba.”

Kara karanta wannan

"Shirin gwamnati ya gaza, " Tsohon gwamnan APC ya fito da matsalolin mulkin Tinubu

"Yana ci gaba da kokarin fitar da kasar daga matsalolin tattalin arzikin da gwamnatin Buhari ta bari, bayan sun kasa hana shi zama shugaban ƙasa.”

Rashin tsaro ya ƙara ƙamari a mulkin Buhari

Onoh ya ce a lokacin mulkin Buhari Arewa maso Gabas, Arewa maso Tsakiya, da kuma Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma ba su iya barci cikin kwanciyar hankali.

"Adadin mutanen da aka kashe a Najeriya kafin mulkin Buhari ya kai 34,972, amma daga lokacin da ya hau mulki, adadin ya haura 98,083 zuwa watan Mayu 2023.
"An kashe mutum 27,311 a wa’adinsa na farko, sannan an kashe mutum 35,800 daga 2019 zuwa 2023," in ji shi.

Onoh ya kuma yi nuni da cewa Najeriya ta shiga sahun kasashe mafi hatsari a duniya, sannan an rage matsayinta a cikin jerin kasashen da ke zaman lafiya.

Gazawar Buhari a bangaren tattalin arziki

Jigon APC ya kuma ƙara da cewa gazawar Buhari wajen magance matsalar tsaro ya hana masu zuba jari daga kasashen waje shigowa Najeriya.

Mista Onoh ya bai kamata Buhari ya ba kansa nasarar da bai samu ba, yana mai cewa akwai alkaluma da ke tabbatar da irin gazawarsa a mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Buhari ya yabi Kayode Fayemi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yabi Kayode Fayemi a sakon da ya aika masa na murnar ƙarin shekara.

Muhammadu Buhari ya ce Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban demokuraɗiyya a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262