Sabon Limamin Abuja Ya Yi Nasiha Mai Zafi ga Malamai Masu Jifan Juna ta Intanet

Sabon Limamin Abuja Ya Yi Nasiha Mai Zafi ga Malamai Masu Jifan Juna ta Intanet

  • Sabon limamin masallacin kasa na Abuja, Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu, ya bukaci malamai da masu wa’azi a Najeriya su hada kai
  • Malamin ya ce sabanin fahimta a addini abu ne da aka saba tsawon lokaci, saboda haka bai kamata ya haddasa gaba da rarrabuwar kawuna ba
  • Sholagberu ya gargadi malamai da su guji yin rigingimu a kafafen sada zumunta, domin hakan yana haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabon limamin Masallacin Kasa na Abuja, Sheikh Abdulkadir Sholagberu ya yi kira ga malamai da masu wa’azi da su hada kai tare da kauce wa rigingimu da rarrabuwar kawuna.

Malamin ya bayyana haka ne yayin hudubar da ya gabatar a Masallacin Abuja a ranar Juma’a, inda ya ce bai kamata bambance-bambancen fahimta su zama dalilin gaba ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan Majalisa ya jiƙa yan mazabarsa da miliyoyin Naira, ya ba su shawara

Limami Abuja
Limamin Abuja ya yi nasiha ga malamai. Hoto: @DukeofBourdilon
Asali: Twitter

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya wallafa a X cewa hudubar ita ce ta farko da malamin ya fara bayan nada shi limanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin da ya fito daga jihar Kwara ya yi tir da yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen sukar juna kan al’amuran addini, yana mai cewa hakan yana kara kawo matsala.

Kira kan hadin kai a tsakanin malamai

Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu ya ce tun fil azal malamai kan samu sabanin fahimta kan wasu batutuwa kamar azumi a watan Sha’aban da bikin ranar haihuwar Annabi (S.A.W).

Ya ce bai kamata sabanin ya haddasa gaba da rarrabuwar kawuna ba, domin hakan na iya raunana hadin kai a cikin al’ummar musulmi.

Hakazalika, ya ce malamai su fahimci cewa duk wani sabani da ke bisa hujja yana kara fahimtar addini da hikima a cikin al’ummar musulmi.

Kara karanta wannan

2027: Kashim Shettima ya fadi yadda ya ke mu'amalantar Atiku a bayan fage

Sai dai ya gargadi cewa idan sabanin ya samo asali daga girman kai, jahilci, ko son kare ra’ayin wasu, to hakan yana haddasa matsala kuma yana rage kimar musulunci.

Illar rigingimu a kafafen sada zumunta

Malam Sholagberu ya bayyana cewa kafafen sada zumunta sun zama filin da ake kai hare-hare ga juna a tsakanin malaman addini.

Ya ce wannan dabi’ar na kara raba kawunan musulmi maimakon ta karfafa hadin kansu, yana mai cewa hakan babbar barazana ce ga ci gaban al’ummar musulmi.

Malamin ya bukaci malamai su kasance masu hakuri da juna tare da fahimtar cewa addinin Musulunci yana karfafa jin kai da yafiya a lokacin da aka samu sabanin fahimta.

Haka zalika, ya bukaci kungiyoyin addini su daina kyamatar juna saboda bambancin ra’ayi, yana mai cewa hakan na kawo tsaiko ga ci gaban al’umma.

Muhimmancin neman gafarar Allah

The Cable ta rahoto cewa Sheikh Sholagberu ya bukaci musulmi da su dage da neman gafarar Allah domin samun saukin halin kuncin rayuwa da ake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

Ya ce hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa da ake fuskanta na bukatar musulmi su koma ga Allah domin samun mafita.

Malamin ya kuma tunatar da musulmi cewa watan Ramadan na kara kusantuwa, don haka su yi amfani da damar wajen yin ibada da kyautata halayensu.

Adam Zango ya yi wa malami raddi

A wani rahoton, kun ji cewa dan wasan fim a Najeriya, Adam A. Zango ya yi raddi ga wani malamin Izala kan fatawar da ya yi game da ridda.

Adam A. Zango ya yi raddi ga Sheikh Salihu Al-Burhan ne bayan malamin ya ce sanya alkyabba a yi rawa na iya fitar da mutum daga musulunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng