Asiri Ya Tonu: An Kama Mutum 9 da Ake Zargi da Hannu a Kisan Ɗan Majalisa

Asiri Ya Tonu: An Kama Mutum 9 da Ake Zargi da Hannu a Kisan Ɗan Majalisa

  • Dakarun ƴan sanda sun yi nasarar kama mutane tara da ake zargin suna da hannu a kisan ɗan Majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka
  • A ranar 24 ga watan Disamba, 2024 ne aka sace Hon. Azuka sannan aka kashe shi a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Kwamishinan ƴan sandan Anambra, Nnaghe Itam ya ce dakaru da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun sheƙe ƴan ta'adda da yawa, sun kwato makamai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Rundunar ‘yan sandan Anambra tare da hadin gwiwar ‘yan bijilanti sun cafke mutane tara da ake zargi da hannu a kashe dan majalisar dokokin jihar, Justice Azuka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nnaghe Itam, ya tabbatar da kama wadanda ake zargi a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Dabara ta fara ƙarewa ƙasurgumin ɗan bindiga, sojoji sun koma maɓoyar Bello Turji

Sufetan yan sanda.
Yan sanda sun kama mutum 9 da ake zargi da kisan ɗan Majalisa a Anambra Hoto: Police
Asali: Facebook

Sacewa da kashe Ɗan Majalisar Anambra

Channels tv ta ruwaito cewa mahara sun sace Justice Azuka, wanda ke wakiltar mazabar Onitsha ta Arewa 1, a ranar 24 ga Disamba, 2024, a birnin Onitsha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa a jiya Alhamis ne aka gano gawarsa da ta fara rubewa a gadar Neja ta biyu, bayan jami’an tsaro da ‘yan bijilanti suka zurfafa bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa an kwato bindigogi guda biyu daga hannun wadanda ake zargi da kisan ɗan Majalisar dokokin.

'Yan sanda sun kama mutane 9 da ake zargi

Har ila yau, CP Itam ya ce daya daga cikin su ya samu raunin harbin bindiga a kafarsa yayin musayar wuta da jami’an tsaro.

Waɗanda ƴan sanda suka kam sun haɗa da Ugochukwu Onuorah (30), Ikemefuna Ossai (20), Ikenna Orugu (27), Chibuike Obiefuna (19), Chinonso Olisa (19), Chinedu Okoli (21)

Sauran su ne David Ojini (25) da kuma Peter Sunday (20) wanda aka ce yana da zane (tattoo) a kirjinsa da ke cewa “ba zaman lafiya ga gwamnati.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a daren Juma'a, mutanen gari sun masu tara tara, an rasa rai

Yan sanda sun murƙushe ƴan ta'adda

Baya ga wadannan mutane tara, kwamishinan ‘yan sandan ya ce an kuma kama wani Chidiebere Nwosu, wanda aka zarga da hannu a garkuwa da mutane a Uruagu, Nnewi.

Nnaghe Itam ya ce rundunar ta hallaka fiye da ‘yan ta’adda 100 tare da rusa sansanonin ‘yan bindiga a Ufuma, Eziowelle, Achalla, Ogbaru da wasu wurare a jihar.

Kwamishinan ya gode wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, da sauran jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula, da jama’a bisa hadin kan da suke bayarwa.

Ya kuma bada tabbacin cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, rahoton Leadership.

Jami'an tsaro sun ragargaji miyagu

A wani labarin, kun ji cewa jami'an tsaron da gwamnan Anambra sun ɗauka aiki sun kai samame a maɓoyar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Matsin lamba daga sojoji ya tilastawa Turji da amininsa tserewa, an fadi halin da suke ciki

An ruwaito cewa dakarun sun yi nasarar fatattakar miyagun, sun kwato mugayen makamai daga hannunsu a musayar wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262