Sojoji Sun Yi Galaba a kan Manyan 'Yan Ta'adda a Zamfara
- Sojojin Operation Fansan Yamma a ƙarƙashin aikin "Operation Show No Mercy" sun kashe shugabannin ‘yan ta’adda da wasu mayaka guda hudu
- Dakarun sun yi zazzafar musayar wuta da yan ta'adda, inda suka kashe ‘yan ta’adda guda shida da kwato babura guda uku da makamai da dama
- Kachalla Gwammade, wanda aka kashe, yana daga cikin dangin Kachalla Sani Black, wani sanannen jagoran ‘yan ta’adda da aka kashe a baya
- Jami'an sun samu wannan nasara ne da haɗin gwiwa da taimakon 'yan sa kai a cikin ƙoƙarin da ake yi na magance ta’addanci a Arewacin Zamfara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Sojojin Operation Fansan Yamma a ƙarƙashin aikin "Operation Show No Mercy" sun kashe manyan ‘yan ta’adda guda biyu; Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai hari a daren Juma'a, mutanen gari sun masu tara tara, an rasa rai
An kashe mugayen jagororin ‘yan ta’addan tare da mayakan su hudu a ƙauyen Ruwan Dawa, a cikin karamar hukumar Maru, Jihar Zamfara.

Asali: Facebook
Mai sharhi a kan al'amuran tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X, cewa aikin ya gudana ne ta hannun sojoji da ke kan hanyar Magami–Dan Sadau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka kashe ‘yan ta’adda
Sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan, inda suka kashe ‘yan ta’adda guda shida tare da kwato babura guda uku da kuma miyagun makamai.
Kachalla Gwammade, wanda aka san shi da jagorancin ta'addanci, yana gudanar da ayyukansa daga wani sansani a ƙauyen Chabi, a Arewa maso Gabas na Maru.
Hakanan, Kachalla Gwammade yana daga cikin dangin Kachalla Sani Black, wanda wani sanannen jagoran ‘yan ta’adda ne da aka kashe kwanan nan a cikin ayyukan soja na yanzu.
Sojoji na samun nasara kan ‘yan ta’adda a Zamfara

Kara karanta wannan
Matsin lamba daga sojoji ya tilastawa Turji da amininsa tserewa, an fadi halin da suke ciki
Wannan nasara ta samu ne a cikin ƙoƙarin da sojoji ke yi na ƙarfafa yaki da ‘yan ta’adda a Arewacin Jihar Zamfara.
An samu wannan nasara ne ta haɗin gwiwa da ‘yan kungiyar sa kai da ke yankin, a kokarin da ake yi wajen fatattakar 'yan ta'adda da ke addabar yankin.
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 358 a cikin watan Janairu 2025, yayin da suka kuma kama 431 da ake zargi da aikata laifuka.
Wannan nasara ta samu ne a cikin ƙoƙarin da sojojin ke yi na yaki da 'yan ta'addan a cikin ƙasar, ciki har da ceto mutane 249 da aka yi garkuwa da su da kuma dakile yunƙurin satar danyen mai a Kudancin Najeriya.
A cikin wannan yaki, sojojin sun kwato makamai 370 da alburusai 4,972 daga hannun 'yan ta'addan, ciki har da bindigogi na AK-47 da bindigogin da su ke amfani da su a kan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng