'Yan Sanda Sun Samu Bayanan Shirin Kai Hari, An Hana Zirga Zirga a Gombe

'Yan Sanda Sun Samu Bayanan Shirin Kai Hari, An Hana Zirga Zirga a Gombe

  • 'Yan sandan Najeriya sun takaita zirga-zirga a Gombe daga karfe 12:00 na dare zuwa 5:00 na asuba saboda barazanar tsaro
  • Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu bayanan sirri cewa bata-gari na shirin aikata laifuka a sassan jihar, wanda ya sa aka ɗauki mataki
  • Kakakin rundunar ya bukaci iyaye su ja kunnen 'ya'yansu domin gujewa karya dokar hana zirga-zirgar da aka samar don kare rayuka
  • DSP Buhari Abdullahi ya ce rundunar ta bukaci jama’a su kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ta lambobin da aka bayar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe - Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta bayyana cewa an samu barazanar tsaro da ka iya yin illa ga rayuwar mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta bullo da sabuwar dabarar kashe bayin Allah, an hallaka mutane a Borno

Saboda haka, rundunar ta dauki matakin takaita zirga-zirga domin dakile wannan barazana.

Buharee Abdullahi Dam Roni
An takaita zirga-zirga a Gombe Hoto: Buharee Abdullahi Dam Roni
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin takaita zirga-zirga a Gombe

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta ce ta samu sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari na shirin aikata ayyukan ta’addanci a sassan jihar.

Sanarwar ta ce:

"A kokarin hana aikata miyagun laifuffuka, rundunar 'yan sanda ta jihar Gombe ta takaita zirga-zirga daga karfe 12:00 na dare zuwa 5:00 na asuba."

'Yan sanda sun shawarci iyaye a Gombe

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta shawarci iyaye da su ja kunnen 'ya'yansu domin gujewa karya dokar hana zirga-zirga.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Rundunar na tabbatar wa al'umma cewa tsaro da zaman lafiyar su shine babban abin da ke gabanta."
"Domin korafin Karta-kwana za'aiya Kiran wannan lambar: 08150567771,09036435359."

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Hoto: An zargi dagaci da sara matashi

A baya, mun ruwaito cewa wani matashi mai shekaru 15 mai suna Adamu Muhammad, ya samu munanan raunuka sakamakon saran adda a unguwar Kagarawal da ke jihar Gombe.

Adamu ya zargi Dagacin Kagarawal, Alhaji Bello A. Usman, da yi masa wannan rauni bisa zargin sata, lamarin da ya bayyana cewa bai yi laifin da ake zarginsa da aikata wa ba.

Sai dai, dagacin ya musanta wannan zargi, ya bayyana cewa ya ji motsin wani yana ƙoƙarin sace masa kayan amfanin gona, ya fito ya tarar da Adamu yana ƙoƙarin guduwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.