Matsalar Albashi: Kungiyar Malaman Najeriya Ta Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
- Malaman makarantun firamare a kananan hukumomi bakwai na jihar Ebonyi sun shiga yajin aiki saboda rashin biyan albashi
- Kungiyar NUT ta ce yajin aikin zai ci gaba har sai shugabannin kananan hukumomi sun biya albashin watanni uku na malaman
- An umarci shugabannin kungiyar a jiha da kananan hukumomi su tabbatar da cikakken bin umarnin yajin aikin na sai baba-ta-gani
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Malaman makarantun firamare a kananan hukumomi bakwai na jihar Ebonyi sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Alhamis.
Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) reshen jihar ta bayyana cewa fara yajin aikin ya biyo bayan gazawar shugabannin kananan hukumomin biyan albashin mambobinsu.

Asali: Getty Images
Kananan hukumomin da abin ya shafa su ne Ebonyi, Edda, Ezza ta Kudu, Ezza ta Arewa, Ivo, Ishielu da Ohaukwu, inji rahoton jaridar Punch.

Kara karanta wannan
An gabatar da bukatar kirkirar sababbin jihohi 31 a Najeriya, an jero su daga yankuna 6
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamai sun tsunduma yajin aiki a Ebonyi
Wani bayani daga sakataren kungiyar, Bassey Asuquo, ya ce yajin aikin ya samo asali ne daga rashin biyan albashin watanni uku ga wasu malamai.
Asuquo ya ce:
“Bayan gargadin farko, mun sake duba matsayin shugabannin kananan hukumomi kan biyan albashin 'yan kungiyarmu.
“Mun gane cewa wasu kananan hukumomi sun cika alkawarin biyan albashin kafin ƙarshen ranar 5 ga Fabrairu, 2025."
NUT ta aika sako ga malaman Ebonyi
Sai dai sakataren kungiyar ya ce har yanzu akwai wasu shugabannin kananan hukumomi da suka yi biris ko suka gaza biyan albashin da ake binsu.
Saboda haka ne kungiyar ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a kananan hukumomin Edda, Ebonyi, Ezza ta Kudu, Ezza ta Arewa, Ishielu, Ivo da Ohaukwu, inji Asuquo.
Kungiyar ta umarci shugabanninta a matakin jiha da rassan kananan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cikakken bin wannan umarni na shiga yajin aiki.

Kara karanta wannan
'Za mu dauki mataki': Abin da Sanusi II ya ce da aka kashe mutane wajen rusau Kano
Malamai sun tsunduma yajin aiki a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman firamare na Abuja karkashin kungiyar NUT sun shiga yajin aiki bayan gargaɗin farko da suka yi wa gwamnati.
Shugaban NUT na Abuja, Kwamared Ameh Baba, ya ce sun fara yajin aikin ne sakamakon rashin biyan su haƙƙoƙinsu da aka rike.
Kwamared Ameh Baba ya kara da cewa cikin kankanin lokaci malaman sakandare za su shiga yajin aikin don nuna goyon baya ga malaman firamare a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng