Gwamnati Ta Rushe Makarantun Sakandare, Ta Kawo Sabon Tsarin Ilimi a Najeriya
- Gwamnatin ta gabatar da tsarin karatun bai daya na shekaru 12, wanda zai kawo karshen tsarin karatun sakandare na JSS, SSS
- Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa wannan tsarin zai rage yawan daliban da ke fita daga makaranta da inganta ilimi
- Gwamnatin tarayyar ta ce sabon tsarin zai kawo cigaba mai dorewa a fannin ilimi, wanda ake sa ran zai dace da bukatun duniya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da soke dukkanin kananan makarantun sakandare (JSS) da manyan makarantun sakandare (SSS) na kasar nan.
Gwamnatin ta gabatar da sabon tsarin karatun bai daya na shekaru 12, wanda zai bai wa yara damar neman ilimin firamare da sakandare a hade.

Source: Getty Images
Gwamnati ta canja tsarin ilimi a Najeriya
Wannan cigaba yana nufin gwamnatin Najeriya na neman kawar da tsarin ilimin 6-3-3-4, sannan ta maye gurbin sa da tsarin 12-4, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, an nemi majalisar kolin ilimi ta kasa (NCE) ta amince da shekaru 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun shiga jami’o’i a kasar.
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, 2025, a Abuja, yayin taron gaggawa na NCE.
Minista ya yi magana a taron NCE
Rahoto ya nuna cewa NCE ita ce hukuma mafi girma da ke yanke shawara a bangaren ilimi a Najeriya.
A wajen taron, an samu halartar kwamishinonin ilimi daga jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT), hukumomi, da kungiyoyi.
A cewar Dakta Alausa, idan an haɗa ilimin sakandare cikin ilimin bai daya, dalibai za su samu damar ci gaba da karatu ba tare da katsewa ba har zuwa shekaru 16.
Gwamnati ta fadi manufar canja tsarin ilimin
Ministan ilimin kasar ya ce sabon tsarin yana cikin sababbin hanyoyin ilimi da ake amfani da su a duniya a wannan zamanin.
Ya ƙara da cewa wannan gyaran zai rage yawan daliban da ke fita daga makaranta saboda matsalolin kudi da tsarin da ke hana su kammala karatu.
“Wannan tsarin zai tabbatar da samun manhajar karatu guda daya wacce za a aiwatar a dukkanin sassan kasar,” inji Alausa.
Ministan ya kuma ce idan ya zamana dalibai suna shafe shekaru 12 kafin shiga jami'a, da shekaru 4 a jami'a, za su samu kwarewar sana'o'i da kirkire-kirkire.
Asali: Legit.ng

