Tsohuwar Minista da Tinubu Ya Kora Ta Koma Harkar Fim, An Jero Fina Finanta
- Tsohuwar Ministar harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta koma harkar fina-finan Nollywood a Najeriya
- Madam Kennedy-Ohanenye ta dawo fim ne bayan sallamarta daga kujerar Ministar gwamnati a watan Oktoba 2024.
- Sabon fim ɗin da tsohuwar Ministar ta fito mai suna Hatred yana ɗauke da fitattun 'yan wasan kwaikwayo
- Kennedy-Ohanenye lauya ce, a 2023, ta tsaya takarar shugabancin ƙasa, amma daga baya ta janye wa Shugaba Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohuwar Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Uju Kennedy-Ohanenye, ta koma shirin fina-finai Nollywood.
Kennedy-Ohanenye ta yanke shawarar shiga fim ne bayan sallamarta a ranar 24 ga Oktobar 2024 daga kujerar minista.

Asali: Facebook
Yadda tsohuwar Minista ta koma fim a Najeriya
Lauyan, wacce ta shirya fina-finai kamar Mama Onboard, The Senator, The Governor, da The President, ta sanar da fitowar sabon fim ɗinta a shafinta na X.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fim ɗin mai suna Hatred yana dauke da jarumai kamar Sorochi Onyekwere da Onyi Maduegbunam da Ifunanya Nwobi da Kachi Obimma.
Bincike ya nuna cewa fim ɗin mai tsawon mintuna 40 da daƙiƙa 6 da ta ɗora a shafinta na YouTube ya samu kallo 1,759 kuma mutane 26 sun yi sha'awarsa.
Kennedy-Ohanenye ta fito a fina-finai kamar Saving My Marriage, Hunting the Angel, Royal Ploy, da The Cow Girls.
Ta yi aiki tare da manyan jarumai irin su Solomon Akiese da Jerry Williams da Segun Arinze da Ngozi Ezeonu da Linda Osifo da Francis Duru.
Tsohuwar minista ta janye takara da Tinubu
A 2023, ta tsaya takarar fitar da gwanin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC amma daga baya ta janye wa Bola Tinubu.
Kennedy-Ohanenye lauya ce mai aiki da kungiyar lauyoyi ta Najeriya, kuma tana harkokin gidaje da ilimi.
A matsayinta na Shugabar Uju Kennedy-Ohanenye, tana ba da ayyukan shari'a ga mutane da kamfanoni.
Bugu da kari, ita ce kafiya kuma shugabar Uju Kennedy-Ohanenye Academy, wata makaranta mai zaman kanta.
Tsohuwar minista ta koma aikinta na kotu
Kun ji cewa tsohuwar ministar mata da walwalar jama'a, Uju Kennedy-Ohanenye ta koma kotu bayan korar ta da Bola Tinubu ya yi mata.
A cikin wani bidiyo, ta bayyana lashi takobin yakar cin zarafi, musamman a shari’o’in da suka shafi ‘yan Najeriya da ke da rauni.
Wakiltar wata yarinya ‘yar shekara biyar da aka ci zarafinta da tsohuwar ministar ta yi ya nuna jajircewarta na ganin an shimfida adalci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng